✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Kofin Nahiyar Turai: Gobe za a fara fafata zagaye na biyu

Gobe Asabar ne za a fara fafatawa a zagaye na biyu na Gasar cin Kofin Nahiyar Turai da ake gudanarwa a kasar Faransa. kasar Switzerland…

 ‘Yan wasan qasar Faransa na murna bayan sun jefa qwallo a ragaGobe Asabar ne za a fara fafatawa a zagaye na biyu na Gasar cin Kofin Nahiyar Turai da ake gudanarwa a kasar Faransa.
kasar Switzerland ce za ta share fage a fafatawar zagayen na kifa daya kwala da kasar Poland a gobe Asabar da misalin karfe 3:00 na yamma, yayin da kasar Wales za ta fafata da kasar Northern Ireland da karfe 6:00 sai kuma
Kuroshiya ta shawo ta da kasar Portugal da karfe 9:00 na dare.
Faransa mai masaukin baki za ta hadu ne da Jamhuriyar Ireland a jibi Lahadi da karfe 3:00 na rana, sai Jamus ta goge raini da kasar Silobekiya da karfe 6:00 na yamma, sai kasar Hungary ta fafata da kasar Beljiyum. A ranar Litinin ce kasar Italiya za ta kece raini da  kasar Spain sai Ingila ta fafata da Iceland.
kasar Faransa ta kai zagayen na biyu ne a matsayi na daya a Rukunin A da maki 7, sai kasar Switzerland ta take wa Faransa baya da maki 5. Faransa ta samu maki bakwai ne bayan ta samu nasara a wasanni biyu da kunnen doki daya, ita kuma Switzerland ta samu maki biyar bayan ta samu nasara a wasa daya ta yi kunnen doki biyu.
A Rukunin B, kasar Wales ta haye ne da maki 6, bayan ta samu nasara a wasa biyu ta yi rashin sa’a daya, sai kasar Ingila ke biye da ita da maki 5, bayan ta lashe wasa daya ta yi kunnen doki biyu. Jamus wadda ita ce Zakaran Kofin Duniya da Poland da ke bi mata sun haye zuwa zagayen na kifa daya kwale ne daga Rukuni na C, bayan da Jamus ta doke Ireland ta Arewa da ci daya mai ban haushi ta hannun Mario Gomez, yayin da Jakub Blaszcykowski da ya shiga wasa bayan dawowa hutun rabin lokaci ya ciyo wa Poland kwallo daya a fafatawar da suka yi da Ukraine a birnin Marseille na Faransa a wasansu na karshe a rukunin, Jamus ta hada maki 7, Poland ma 7. Kuroshiya ta ba Spain mamaki ta hanyar jagorantar Rukunin D da maki 7, Spain na bin ta da maki 6.  A  Rukunin E, Italiya ce ke a gaba da maki 6, sai Beljiyum ke bi mata da maki 6. Rukunin F, kasar Hungary ce ja gaba da maki 5, sai kasar Iceland ke bin ta da maki 4. Sai kuma wasu kasashe da suka samu gurbi zuwa zagayen na biyu sakamakon hada maki daidai da wadanda suka zo na biyu, wadanda suka hada da Slobakia da Ireland ta Arewa da Portugal.