✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar City People: Momo da Kamal da Umar M Shareef sun haskaka a Legas

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka gabatar da bikin bada lambar yabo ta City People Entertainment Award a birnin Legas. Gasar City People…

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka gabatar da bikin bada lambar yabo ta City People Entertainment Award a birnin Legas.

Gasar City People ana bayar da ita ne ga wadanda suka taka muhimmiyar rawa a bangarori da dama na sana’ar fim da wake-wake.

Ita wannan lambar yabo ana gabatar da ita ne duk shekara a birnin Legas.

A gasar ta bana jarumi Aminu Sharif Momo ne ya zama Gwarzon jarumi, bayan ya fafata da jarumi Adamu A. Zango da Yakubu Mohammed da Ali Nuhu da Sadik Sani Sadik da Suleiman Basho da kuma Rabi’u Rikadawa

Lawan Ahmad ya kasance Mai tallafa wa Gwarzon Jarumi, bayan ya faffata da Nuhu Abdullahi da Abdul M shereef da Haruna Talle Mafata da Rabi’u Daushe da kuma Rabi’u Rikadawa

Darakta Kamal S. Alkali she ne ya zama Gwarzon Darakta, sakamakon hazakar da ya nuna a lokacin da ya bada umarni a fim din ‘Umar Sanda’.

A wannan rukunin daraktan ya fafata da Yaseen Auwal da Hassan Giggs da Falalu Dorayi da Sadik Mafiya da kuma Ali Gumzak ne.

Ibrahim Daddy shi ne Gwarzon Jarumi a bangaren fina-finan da ake nuna wa a talabijin, inda Umar M. Shareef sakamakon rawar da ya taka a fim din ‘Mansoor’ ya lashe kambin Gwarzon Jarumi Mai Tasowa.

Hajara Isa Jalingo jarumar fim din ‘There’s A Way’ da ‘This’s the Way’ da kuma ‘Light And Darkness’ ta lashe kyautar Gwarzuwar Jaruma mai Tasowa’.

Hajara ta lashe kyautarta ne bayan ta fafata da Sadiya Kabala da Sadiya Adamu da Maryam Yahaya da Maryam Gana da Asabe Madaki da kuma Maryam Aliyu ’Yar fim

Aisho Labbo ce ta zama Gwarzuwar Jaruma a bangaren fina-finan da ake nuna wa a talabijin. Shirin ‘Kukan Kurciya’ da ’Yan Zamani’ da kuma ‘Mairo’ da ake nuna wa a gidajen talabijin ya ba jarumar farin jini, inda rol din da taka a cikinsu ya sanya ta kai ga nasarar da cimma. 

Sani Sule, mai kamfanin Rite Time, wanda ya shirya fim din ‘Sarauniya’, ne ya lashe kyautar Gwarzon Furodusa, bayan ya fafata da Abdul Amart da Abubakar Bashir Maishadda da Naziru danhajiya da Musa Jammaje da kuma Ibrahim Jidawa.

Maryam Aliyu ita ce ta lashe Gwarzuwar Sabuwar Jaruma, inda Ali Nuhu aka karrama shi da dan fim mafi samun nasara a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.

Ahmad Ali Nuhu shi ne Gwarzon Jarumi a rukunin yara, inda muhimmiyar rawa da ya taka a cikin fim ‘dan Almajiri’ ya ba shi wannan nasarar da ya cimma.

A lokacin da yake jawabi, Darakta Kamal S. Alkali ya bayyana farin cikinsa bisa ga nasarar da ya samu ta lashe kyautar Gwarzon Darakta.

“Yau rana ce ta farin ciki, domin hakan ya nuna mini ana lura da abin da nake yi, wadda ya kai ga an karrama ni, wannan rana ta zama tarihi a gare ni.” Inji shi.

Daraktan wanda ya shirya manyan fina-finai kamarsu ‘Gaba Da Gabanta’ da ‘Jarumin Maza’ da kuma ‘Jamilun Jidda’ ya ce wannan lambar yabo da ya samu, za ta dada masa kaimi wajen ci gaba da shirya fina-finan da za su ci gaba da ilimantarwa da nishadantarwa da kuma fadakar da masu kallo.

Jaruma Hajara Isa Jalingo a lokacin da take jawabi sai ta fara kabbara, sannan ta mika godiyarta ga Allah bisa ga nasarar da Ya ba ta, ba tare da wayonta ko dabararta ba.

“Allahu Akbar, Alhamdulillah, ina gode wa Kabiru Jammaje da Falalu dorayi bisa ga damar da suka ba ni hade jajircewa wajen fito mini da hazakata, ta dalilin gudunmuwarku ne na lashe kyautar Gwarzuwar Jaruma mai tasowa,” inji ta.

Jarumar ta bayyana cewa ba za ta manta da jarumi Sadi Sawaba ba, inda ta dalilinsa ta shiga harkar fim har ta kai ga lashe kyautar.

A nasa jawabin mawaki kum jarumi Umar M Shareef ya sadaukar da kyautarsa ga jarumi Ali Nuhu.

“Fim din da ya sanya na samu wannan nasarar shi ne fim din ‘Mansoor’, kuma Ali Nuhu shi ne Daraktan wannan fim din, shi ne ya fito da ni har na samu nasara a fim din, don haka ina sadaukar da wannan kyauta gare shi,” inji Umar.