Assalamu alaikum warahmatullah. A makon shekaranjiya ne muka fara gabatar da wannan makala mai taken: “Gare ki uwar ’ya’ya” inda muka tattauna kan koyar da yara dabi’ar GASKIYA To yau za mu ci gaba daga kan wata kyakkyawar dabi’ar wato AFUWA.
Ya ke uwar ’ya’ya! Ki siffantu da dabi’ar afuwa kuma ki koya wa ’ya’yanki dabi’ar afuwa. Afuwa daya ce daga cikin kyawawan dabi’u na Musulunci. Afuwa ita ce mutum ya yafe wani hakki nasa ya yi kyautar wannan hakki cikin karimci da kyautatawa alhali yana da ikon da zai yi ramuwa. Yana yin haka ne don kyautatawa da nuna halayen girma da neman lada a wurin Allah.
Misali wani yaro ya zalunci danki, sai ya zamo dan naki ya yafe alhali zai iya rama wannan zalunci. Shin kina koya wa ’ya’yanki irin wannan dabi’a?
Allah Madaukaki Wanda Ya siffanta kanSa da wannan siffa ta AFUWA ne Ya yi umarni da a yi afuwa kuma Ya kwadaitar kan mutane su rika yin afuwa a ayoyi da dama a cikin Alkur’ani Mai girma. Ya ce: “Da ka kasance mai kaushi da zafin zuciya da sun gudu daga gare ka. Don haka ka yi musu AFUWA kuma ka nema musu gafara…” (Al-Imrana:159).
Afuwa tana daga cikin dabi’un Annabinmu Muhammad (SAW), shi ne shugaban dukkan masu yin afuwa, shi ne mafi tausayin masu tausayi (SAW).
Hakika an siffanta Annabi (SAW) da mutum mai afuwa da yafiya a cikin littattafan da suka gabata, kamar yadda ya zo kan siffarsa (SAW) a cikin Attaura: “Ya kai Annabi! Lallai ne Mun aike ka kana mai bushara da gargadi da kiyaye umiyyin. Kai bawaNa ne kuma ManzoNa. Na yi maka suna da Muwakkil (wanda ake wakiltawa), kai ba mai kaushi da zafin zuciya ba ne, kuma ba mai damfaruwa a kasuwanni ba ne. Kuma ba ya tunkude mummuna da mummuna, amma yana AFUWA ya yi yafiya…” (Buhari).
Kuma Annabi (SAW) ya fada wa Ukubatu bin Amir (RA) lokacin da ya tambaye shi kan ayyuka mafiya falala sai ya ce: “Ya Ukbatu! Ka sadar da zumunta ga wanda ya yanke maka, ka ba wanda ya hana ka, kuma ka yi AFUWA ga wanda ya zalunce ka.” (Ahmad).
Ya ke uwar ’ya’ya! Ki daure ki rika yin afuwa ga ’ya’yanki sai su ma su kwaikwayi yin haka ga wadanda suka saba musu ko suka zaluce su. Kada ki ce duk lokacin da yaro ya yi laifi sai kin buge shi ko sai kin hukunta shi. Ba dabi’ar kirki ba ce, kullum uwa ta rika hayagaga tana sai na ci abu kazanka, sai na doke ka sai na yi maka kaza da kaza! Yaro ya taso ya ga mahaifiyarsa tana kawar da kai daga rashin kyautatawar da shi ya yi mata, ko wani ya yi mata ko abokiyar zama ta yi mata ko makwabta suka yi mata, zai iya koyi da hakan a rayuwarsa ta gaba. Amma wadansu iyaye mata yara ne za su yi fada a yayin da suke wasansu na yara sai su dauki gyale ko hijabi su tafi gidan iyayen abokan wasan dan suna bambami da kashedi kila ma da barazanar zuwa ga hukuma. Da yawa a irin wannan hali ne sai kuma a ji yaran sun koma fagen wasa suna wasansu.
Don haka koda da niyya ko da gayya mutum ya yi wa danki ba daidai ba, ki yi hakuri ki yafe musamman a laifin da za ki iya ramawa, hakan zai sa dan naki ya fahimci amfanin afuwa, shi ma sai ya rika yi ga na kasa da shi.
Ya ke uwar ’ya’ya! Yin afuwa ibada ce kamar yin Sallah. Akwai lada da sakamako a kan yi afuwa. Musulmi duk abin da ya yi don bin umarnin Allah da koyi da Manzon Allah (SAW) ibada yake yi da zai samu lada a gobe Kiyama.
Baya ga haka ki sani ya ke uwar ’ya’ya! Yin afuwa ma yana da nasa alfanun ga ke kanki da wadanda kika koya musu daga cikin ’ya’yanki. Daga cikin abubuwan da afuwa take gadarwa akwai:
1. Afuwa tana gadar da takawa: Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ku yi AFUWAR shi ne mafi kusanci da takawa.” (Bakara: 237). Idan kuwa afuwa za ta kusantar da mutum zuwa ga takawa, takawa kuwa ita ce linzamin shiga Aljanna babu mai shigarta sai mai ita. Shin ba ki son ki shiga Aljanna ce ko kuwa ’ya’yanki ne ba ki son su shiga Aljanna?
2. Afuwa tana wajabta samun gafara: Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma domin su yi AFUWA su yi yafiya. Shin ba ku son Allah Ya yi muku gafara ne?” (Nur:22). Babbar magana, a ce Mahalicci ne Yake shilar cewa “Shin ba ku son Allah Ya yi muku gafara ne!” Lallai wadanda suke kin yin AFUWA da yafiya ya kamata da jin wannan shela su kadu hankalinsu ya tashi su sauya tunani. Na tabbata babu uwar da za ta ce ba ta son Allah Ya gafarta mata, babu uwar da za ta ce ba ta son Allah Ya gafarta wa ’ya’yanta. Don haka ya ke uwar ’ya’ya! Idan kina son Allah Ya gafarta miki ke da ’ya’yanki to ki lizimci yin AFUWA kuma ki koya wa ’ya’yanki yin afuwa ga wadanda suka cutar da su kuma suke da ikon ramawa.
3. Afuwa tana jawo babbar lada a wurin Allah: Allah Madaukaki Ya ce: “Wanda ya yi AFUWA kuma ya gyara, to ladarsa tana wurin Allah.” (Ashhura:40). A wannan aya Allah bai fadi yawan ladar ba, kuma kowa Ya san Allah Mai kyauta ne ba da lissafi ba idan Ya ga dama. Don haka tunda Ya ce ladar mai afuwa tana wurinSa, to uwar ’ya’ya ki yi kokarin ki koya wa ’ya’yanki yin afuwa don su rika girbar wannan lada a nan duniya kuma in sun koma ga Allah su girbi mai yawa a wurin Allah.
Ya ke uwar ’ya’ya! Ba gazawa da kasawa ba ne a zalunci danki ki kawar da kai. An fi son ki kawar da kai ki yafe a lokacin da kike da karfi da ikon da za ki iya daukar fansa. Wannan shi ne hakikanin afuwa, shi ne ke haifar da takawa da samun gafara da babbar lada a wurin Allah.
Allah Ya taimake mu wajen dora ’ya’yanmu a kan halayen kwarai na Musulunci.
Sai makon gobe insha Allah.