✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

GANI YA KORI JI: Hotunan muhimman abubuwa da suka faru a wannan mako

Ga hotunan wasu hotunan abubuwan da suka faru a wannan mako da muke bankwana da shi domin kayatar da ku:     

Ga hotunan wasu hotunan abubuwan da suka faru a wannan mako da muke bankwana da shi domin kayatar da ku: 

Yadda wani makiyayi ya ke tafe da garken tumakinsa akan hanyarsa ta zuwa ba su ruwa a kauyen Bandai na kasar Indiya. Hoto: Prakash SINGH / AFP
A nan kuma hoton wani mutum ne yana tafiya cikin busasshen tabo da tsattsage bayan ruwa  ya janye a wani yanki na kauyen Bandai  lokacin yanayin tsananin zafi a kasar Indiya. Hoto: Prakash SINGH / AFP.
Yadda wata damisa ta buga wawar hamma lokacin da ta ke tsaka da hutawa a cikin kejinta a gidan shakatawar Ayub
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje lokacin da ya ke wa Tinubu maraba da sauka yayin ziyarar da ya kai jihar a ci gaba da neman goyon bayan daliget gabanin zaben fidda gwani na Jam’iyyar APC.

 

Yadda tsohon dan wasan kwallon kafar Kamaru, Patrick Mboma, ya karbi addinin Musulunci a wani masallaci da ke birnin Duoala na kasar inda ya canza sunansa zuwa Abdul Jalil Mboma.

 

Jaririn da shahararriyar mawakiyar Amurka kuma mai kamfanin kayan alfarma na Fenty, Rihanna ta haifa a ranar Alhamis.
Yadda Kwankwaso da mukarrabansa su ka kai wa Obasanjo ziyara a gidansa a ranar Juma’a.                                                                                   Hoto: Ibrahim Adam