Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba, ya ce Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, zai gabatar da ma’aikatan ofisoshin sabbin sarakunan masarautun Gaya da Rano da Karaye da masahrautar Bichi. Wadanda suka haada da: Alhaji Tafida Abubakar Ila (Rano), Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya (Gaya), Dakta Ibrahim Abubakar ll (Karaye) da Alhaji Aminu Ado Bayero (Bichi).
A yau zai gabatar da ma’aikatan ofis na masarautu biyu sauran biyu kuma sai gobe Litinin.