Gwamnatin Jihar Kano ta dauki nauyin biyan Naira miliyan 130 don tallafawa dalibai sama da 10,000 da suka fadi jarabawar ‘Qualifying’ a jihar.
Kwamishinan Kananan Hukumomin Jihar, Murtala Sule Garo ne ya bayyana hakam jim kadan bayan ganawa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a ranar Lahadi.
Garo, ya ce gwamnan jihar ya bada umarnin zabar dalibai 200 daga kowace karamar hukuma 36 da ke kauyukan jihar, sai dalibai 400 daga kananan hukumomi takwas da ke cikin kwaryar birnin Kano.
“Gwamna ya bada umarnin biya wa dalibai ’yan asalin Kano sama da 10,000 da ba zasu iya biyan kudin jarabawar ba,” a cewar Murtala Garo.
Kwamishinan ya ce ana sa ran kowace karamar hukuma za ta kafa kwamitin da zai sa ’yan asalin Kano cin moriyar tallafin.
Idan ba a manta ba, iyaye da dalibai da dama sun bayyana damuwarsu kan yadda aka samu faduwar jarabawar da yawa a bana a fadin jihar.
Gwamnatocin jihohi sun dauki tsawon shekaru suna daukar nauyin biya wa daliban da suka ci jarabawar kudin zana jarabawar NECO.
Sai dai yanayin ya sha bamban da kowace shekara a jihar Kano, inda wajen kaso 90 cikin 100 na daliban jihar suka fadi, sannan aka bayar da kankanin lokaci don biyan kudin jarrabawar NECO wanda zai kai N12,000 zuwa N13,000.