✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya kaddamar da manyan baburan kama masu laifi a Kano

Hukumar KAROTA ta mallaki babura 25 domin kama masu laifi cikin hanzari.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya kaddamar da wasu sabbin Babura 25 da Hukumar KAROTA mai Kula da zirga-zirgar ababen hawa ta tanada domin tabbatar da an kiyaye dokoki a Jihar.

Da yake kaddamar da sabbin Baburan a ranar Lahadi a Fadar Gwamnatin Kano, Ganduje ya ce za a yi amfani da su wajen tabbatar masu zirga-zirga da ababen hawa a kan tituna sun kiyaye dukkanin dokokin da suka dace.

Ya ce baburan za su taimaka wa jami’an KAROTA wajen gudanar da ayyukansu cikin hanzari domin gano masu karya doka sannan su kuma ba su damar kai-komo wajen kama masu shigo da haramtattun kayayyaki cikin Jihar.

Gwamnan ya bukaci jami’an KAROTA da su rubanya kokarinsu na kula da zirga-zirga tare da cafke wanda ke saba wa dokokin hanya.

Ya kuma bukaci su tabbatar da cewa an gano wadanda ake zargi suna dauko dakon kayan da suka saba wa doka.

Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa, Ganduje ya yaba wa Shugaban Hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan Agundi dangane da wannan shiri na sayen baburan da Hukumar ta yi da kudaden da ta tara bayan zare ma’aikatan bogi daga cikinta.

“A wasu lokutan, mukan ga abubuwa yawa na faruwa a kan hanya, mukan ga masu laifi suna dauke da abubuwa a cikin motocinsu amma babu ababen hawa da za mu iya bibiyar sahunsu cikin sauri domin gano inda suka nufa.

“Sai dai a yanzu da muka mallaki wadannan ingatattun Babura na zamani,  za mu iya kama masu laifin cikin hanzari, a cewar Dan Agundi.