✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ka yafewa Sarki Sanusi – Shehu Sani

Tsohon dan majisar dattawan Najeriya da ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya yi kira ga gwamnan Kano da ya kawo karshen…

Tsohon dan majisar dattawan Najeriya da ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya yi kira ga gwamnan Kano da ya kawo karshen rikicin da ke tsakaninsa da sarkin Kano.

Sanata Sani ya bukaci Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ya yafewa Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, sannan ya manta da abin da ya faru.

Shehu Sani, ya kara da cewa, “Ka manta, ka yafe, ka bar Sarki ya ci gaba da rike masarautarsa. Ba a dorewa a kan mulki, wataran za ka bukaci taimakonsa lokacin da na gindinka suka barka”.

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da Sarkin Kano Muhammdu Sunusi II

Tsohon Sanatan ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter.

An dade ana  takun-saka tsakanin Sarkin da Gwamnan, lamrin da ya kai ga Ganduje ya tsattsaga masarautar zuwa gida biyar, abin da sarkin da wasu da dama suka kalubalanta a gaban kotu.

Duk da cewa wasu dattawan kasa na kokarin shiga tsakani, da alama har yanzu ba a kai ga yin cikakken sulhu ba.