Ana sa ran Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsat da wasu mutum shida za su bayyana a gaban kotu a Jihar Kano.
Ana sa ran za su bayyana a gaban kotun da ke tuhumarsu da almundahana a ranae Alhamis.
- An kama ’yan talla da ke kai wa ’yan bindiga bayanai
- An ceto ’yar shekara 2 da maƙocinsu ya sace ta a Kano
Ana zarginsu da cin hanci da almundahanar biliyoyin kuɗaɗe.
Gwamnatin Jihar Kano ta NNPP ce, ta shigar da su ƙara a gaban Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu.
A ranar 5 ga watan Yuni, kotu ta bai wa masu gabatar da ƙara izinin aike wa da waɗanda ake ƙara sammaci ta hanyar tallace-tallace ko jaridu, wanda kuma tuni aka wallafa a ranar 6 ga Yuni a jaridun Daily Trust da The Nation.
Waɗanda ake ƙara su ne Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat, Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, kamfanin Lamash Properties Limited, Safari Textiles Ltd, da Lesage General Enterprises.
A zaman kotun da ya gabata, lauya mai kare wanda ake tuhuma na shida, Nuraini Jimoh SAN, kaɗai ne ya halarci zaman kotun.
Sauran waɗanda ake ƙara, ciki har da Ganduje, ba su aike da wakilci ba.
Mai Shari’a Amina Adamu ta sanya ranar 11 ga watan Yuli domin ci gaba da shari’ar.