✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganawar Trump da Kim: Yadda aka tashi ba tare da matsaya ba

A daren Laraba ce Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un suka sake ganawa karo na biyu a birnin Hanoi…

A daren Laraba ce Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un suka sake ganawa karo na biyu a birnin Hanoi na kasar Bietnam da nufin samun matsaya a kan shirin kasar Koriya ta Arewa na nukiliya, wanda kasashen duniya ke kokarin ganin ta dakatar.

An tashi taron ne a wannan karon ba tare da samun wata matsaya ba, domin Amurka ta ki amincewa da bukatar Shugaba Kim ta a cire wa kasarsa dukan takunkumin da aka kakaba mata.

Wannan bukatar ce ta yi wa Shugaba Trump nauyi, inda ya ce ya kamata ne a ce shi ma Shugaba Kim ya fara kokarin tsayar da shirin da yake yi na samar da nukiliya din, ba wai kawai maganar cire takunkumin ba.

“Wani lokaci dole a ga aiki a zahiri,” a cewar Shugaba Trump lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawar.

Ita dai ganawar da ake tunanin za a zauna ne a daddale batun nukiliyar kasar Koriya ta Arewa, shirin da ke barazana ga yankin Asiya da duniya baki daya da kuma batun cire takunkumin da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka kakaba wa Koriya ta Arewa, an tashi cikin sauri, wanda abin ya ba da mamaki sosai ganin cewa babban taro ne da duniya baki daya ke jiran sakamako, daga baya kuma aka samu labarin cewa ba a samu matsaya ba.

Trump ya bayyana cewa ba ya gaggawar shiga wata yarjejeniya da Koriya ta Arewa domin har yanzu kasar ba ta tsayar da shirinta na nukiliya ba.

“Na sha fada cewa ba a bukatar gaggawa a wannan lamarin,” inji Shugaba Trump da asubahin jiya Alhamis bayan an kammala taron. “Abin da yake da muhimmanci shi ne mu samu matsaya da ta dace,” inji shi.

Sannan kafin Trump ya bar kasar ta Bietnam ya bayyana wa manema labarai cewa babu maganar ganawa ta uku yanzu, amma yana tunanin Kim zai daina gwada makamansa masu linzami.