Zuwa ga Edita hakika ganawar da Gwamnan Jihar Jigawa yayi da Gwamnan Jihar Ribas Mista Amaechi ya nuna lallai ruwa sun kusa kare wa dan kada, domin duk abin da ka ga ya koro kusu, ya fada wuta, to ya fi wutar zafi. Yanzu Sule Lamido ya gano inda akalar siyasar Najeriya ta dosa shi yasa yanzu yake kame-kamen hada hulda da kamfem Coodineta na Janar Buhari, to mu yanzu nasarar ka guda ce ka daina yi wa mutanen Arewa surutu da kazafi na dole su ba ka girma. Domin ba ka da shi tun farko, sauran da ya rage ka ida zubar da abinka a gaban duniya saboda haka idan har kana da niyar dawowa cikin rigar mutunci a cikin talakawan Arewa kawai ka kame bakinka daga yi wa mutane sharrin da kazafi. Domin kawai an ki abin da kake so, kuma ire-irenku sai sun gani da idanun su, za su riga rana faduwa nan kwanaki kadan. Daga Usman Adamu. 07061594299.
Sakonnin waya
Ga sufeto Janar
Salam Aminiya. Zuwa ga Sufeto Janar Sule iman abba wane bincike za ka yi a kan su Dakubo Asari, tsagerun Neja-Dalta, bayan duniya ta ji abin da suka fada, in Jonathan bai ci zabe ba, za a yi yaki. Haka suka fada kuma ka ce za ku kama ’yan bangar siyasa. Ko don sun ce Jonathan ne Ogan su kake jin tsoron kama su. Ka ji tsoron Allah, akwai Lahira, kai Musulmi ne. daga Hayatu Basheer Abuja 07050516893.
Ga Aminan Aminiya
Edita ka ba ni dama in isar da fatan alheri ga ’yan makarantar Dodorido da Aminan aminiya, wadanda suka hada da Aunty Halima Shata da Uncle Bash da Hajiya Sadiya Bachirawa da Alhaji Ibrahim na Shehu Zariya. Shi ma Bashir Yahuza da mutanensa, tare da sauran aminan Aminiya. Daga Auwalu Yayan Fati 08152073868.
Arewa ce saniyar ware
Munafunci dodo yakan ci mai shi. Shugaba Jonathan ka je Maiduguri, sai ga shi bom ya tashi a Gombe. Mun san an mayar da Arewa saniyar ware. Allah ya kaimu ranar zabe. Duk mai bakin ciki ba zai dauwama da larura ba. Daga Usman Bala 07037084451.
Me zai hana hutun zabe?
Edita don Allah ka ba ni dama in yi tsokaci dangane da matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na kin rufe makarantu a lokacin gudanar da zaben kasa, hakkika akwai ayar tambaya akan wannan mataki ganin yadda kasar nan ke cikin halin barazanar tsaro bayan haka, mu talakawa mun lura da matakai na yin magudi a lokacin zabe muna sane da cewa da dama daliban makarantun nan suna da rijistarsu, wadda za su yi amfani da ita kuma da dama sun yanki katunansu ne a unguwanninsu. Don haka muke ganin ta yaya za su iya amfani da damarsu wajen zaben ra’ayinsu ya kamata gwamnati ta sake duba wannan matakin wajen bai wa daliban hutu domin su dawo gida su yi zabe. Daga Aminu Abdu Baka Noma, Sani Mainagge, Kano 08099479880.
Ga Hukumar Zabe
Assalamu alaikum Edita, don Allah ku mika min kirana zuwa ga hukumar zabe ta kasa INEC, ya kamata hukumar ta fito da wani tsari da zai bai wa ‘yan uwanmu na jihohin Yobe da Borno da yanzu haka ke zaune a wasu jihohi sanadiyar rikicin Boko Haram, kasancewar sun bar gidajen na su ne ba da son ransu ba, sai don kaddara da kuma gazawar gwamnati na daukar matakan da suka dace don yakar ‘yan ta’addar Boko Haram, da fatan INEC za ta dubi wannan kiran namu da idan basira. Domin su samu su kada kuri’unsu, a matsayinsu na ‘yan kasa. Daga Usman Bin Affan damaturu a Jihar Yobe 08038001563.
Mu zabi nagarta
Matasan Najeriya mu nema wa kanmu mafita daga amfani da yan’siyasa ke yi da mu wajen biyan bukatun su, da sun ci zabe su manta da mu. Mu jajirce wajen ganin mun zabi nagartaccen dan’takarar da jibinci lamuran mu da matsalolin mu. Mu guje wa gurbatattun ’yan siyasa masu lalata rayuwar mu, ta hanyar shayar da mu miyagun kwayoyi da ba mu makamai don biyan bukatun su na siyasa. Kowa yasan dan takarar da ya cancanta a zaba, tun daga matakin shugaban kasa har yan’majalissar jihohi. Kar mu yarda a rude mu da abin da bai kai ya kawo ba, a ci gaba da jefa rayuwar mu cikin fargabar kisan gilla da tsadar rayuwa da rashin aikin yi da cin hanci da rashin tituna da wutar lantarki da ruwan sha. Allah Ya kawo mana sauyin rayuwa mai alfanu. Amin. Daga Mansoor Said PRP Kano. 07039215954.
Katobarar Shema da Yero
Edita hakika katobarar Gwanonin Katsina da na Kaduna sun jefa mutanen cikin mamaki. Gwamna shema dai ya ce ’yan adawa kyankyasai ne, a masai suke, to a ku buge su. Shi kuwa Gwamnan Kaduna Ramalan Yero, ya yi tasa katobarar, inda yake cewa’duk wanda uwarsa ta haife shi! Duk wanda uwarsa ta haifeshi !! Duk wanda uwar shi ta haifeshi!!! Idon shi gwamnan da tawagar sa sun fito kamfe to ya gwada jifar su ko ya kona musu mota zai ga abin da zai biyo baya ba mutun cin su ba ne aji bakunan su suna fitar da irin wadannan kalamai. Allah Ubangiji ya ba mu shugaban ni nagari. Daga Haruna Muhammad Katsina. 07039205659.
Ta’aziyyar Sarki Abdallah
Ina mika sakon ta‘aziyyata ga kasar Saudiyya, dangane da rasuwar mai martaba Sarki Abdallah bn Abdulaziz, wanda Allah yayiwarasuwa makon da ya gabata. Da fatan Allah yajikansa, ya gafarta masa ya sanya Aljanna ta zamo mako a gareshi. Daga karshe nake taya sabon Sarkin Salma Bn Abdulaziz murnar hawa wannan mukami. Da fatan Allah ya tayashi riko.
Daga: Isah Ramin Hudu, Hadejia. 08060353382.
Addu’a ce mafita
Jama’a mu yi addu’a saboda karatowar zabe. Mu daina surutu mara ma’ana. Daga Binta Manzo Daura 08169230847.