✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gamayyar kungiyoyin nakasassu ta nemi gwamnonin Arewa su tallafa wa ’ya’yanta

Gamayyar kungiyoyin nakasassu ta Jihar Bauchi ta yaba wa gwamnatin jihar kan tallafin da take ba ta, lamarin da ya sa ta roki shugaban kungiyar…

Gamayyar kungiyoyin nakasassu ta Jihar Bauchi ta yaba wa gwamnatin jihar kan tallafin da take ba ta, lamarin da ya sa ta roki shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Alhaji Babangida Aliyu kan ya yi hudubar musamman ga sauran gwamnoni domin su bi irin wannan sahu wajen tallafa wa nakasassu, domin a samun nasarar hana yawon barace-barace.
Shugaban kungiyar makafi na jihar, wanda kuma shi ne sakataren gamayyar kungiyar nakasassu na Afirka, Alhaji Abdullahi Jibrin shi ne ya bayyana haka a lokacin da ake raba musu tallafin buhuna dubu goma da suka kunshi na shinkafa da gero da dawa da suga, wanda Gwamna Malam Isa Yuguda yakan raba musu bayan kowane watanni uku.
Sakatare Abdullahi ya ce wannan tallafi babban al’amari ne, wanda suke ganin amfaninsa, lamarin da ya sa musakai tattaruwa waje guda domin ganin sun ci gajiyar tallafin yadda ya dace. Hakan kuma ya sa mabarata suka ragu a Jihar Bauchi a daidai wannan lokaci da wasu jihohi ke korar nakasassun daga jihohinsu.
Ganin yadda gwamnati ke lura da su, nakasassun sun tsara kansu suna sana’o’in da za su iya, yayin da masu sha’awar bara kuma saboda ganin tallafin ya yi musu kadan saboda yawan iyali, yawanci suna zama waje guda ne, kamar a bakin masallatai ko shatale-tale domin neman kari.
Ya ce saboda gwamnati ta gansu cikin tsari, ba ta matsa musu, sai ko kara musu yawan kayan abincin take yi. Saboda a baya ana ba su buhunna dubu takwas ne, sai aka koma dubu tara, yanzu an mayar dubu goma cikin watanni shida. Yanzu kuma a wannan karo cikin watanni uku an sake kara musu buhu dubu goma. Don haka ya bukaci kowane mutum ya lura da yadda nakasassu suke gudanar da hidimominsu cikin tsari a Jihar Bauchi, kuma shi ne ya sa ba mai matsa musu saboda suna bin doka kuma ana ba su tallafin da ke rike su. Don haka su ma suke kokari wajen ganin an raba kayayyakin abincin a dukkan kananan hukumomi 20 na jihar ba tare da wani korafi ba, haka kuma su ma a kullum suna addu’ar fatar alheri tare da rokon Allah domin samun zaman lafiya a Jihar Bauchi da Najeriya baki daya.
Daga nan kuma ya yaba wa shugaban kungiyar gamayyar ’yan kasuwa na Jihar Bauchi, Alhaji Salisu Garba Maisuga, wanda aka dora masa alhakin raba musu kayayyakin, game da yadda yake rike amanar da aka dora masa, “Musamman saboda a wasu lokutan ko lokacin ba mu kayan bai yi ba, shi ma da kansa yana saya ya raba mana domin neman yardar Allah”. Inji shi. Sannan ya roki Gwamna Malam Isa Yuguda ya yawaita irin wadannan mutane a cikin gwamnatinsa tare kuma da gina mutanen kirki da za su gaje shi saboda su ci gaba da cin wannan moriya ko da bayan ya gama mulkinsa.
Shi ma shugaban gamayyar kungiyoyin nakasassu kuma mai rikon Sarkin Guragu na Bauchi, Alhaji Ali Abdullahi Shongo ya ja hankalin masu hannu da shuni da gwamnatin Goodluck Jonathan su samar da wani asusu na musamman domin tallafa wa nakasassun kamar yadda ake yi a Jihar Bauchi, domin shi ne zai taimaka wajen rage matsalar bara da almajiranci da ake fama da shi a wannan lokaci.