✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ga Sheikh dahiru Bauchi da Ahmadu Mai dankoko

Editan Aminiya, ka ba ni dama in mika sako ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Sheikh Ahamadu Mai dankoko, wanda ni a matsayina na mai…

Editan Aminiya, ka ba ni dama in mika sako ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi da Sheikh Ahamadu Mai dankoko, wanda ni a matsayina na mai karanta wannan jarida ta Aminiya nike fatan don Allah wanda muke bauta wa da neman taimakonSa da dacewar shi ayi takatsantsan, wajen maida martani, a fahimci juna a cikin Musulunci da akwai sauran wasu mabambantan akidu. Shin sai darika da Izala za a yi ta zafafan kalamu? don Allah a yi hakuri, Daga Mukhtar Ibrahim saulawa. katsina 08080140820-07066434519

Sakonnin waya

Yabo ga gwanayen Sakkwatawa
Yabon gwani ya zama dole, don Allah ku dawo a shekarar 2015. Hon. Abdu Hassan mun gode da Hon. Amin Bodi, Sakkwatawa sun gode. Gwamna Wamako ya gode. Daga Alhaji Murtala M. Kanuri Sarki Shatima Sharfi Sakkwato 08030832849.

Rabonku da sakona tun 2013
Salam Editan Aminiya mai farin jini, tun 2013 baka sake rubuta sakona ba, shi yasa a 2014 na yi sammakon turo, don gaisuwa ga aminan Aminiya, da taya su murnar shiga sabuwar shekarar miladiyya. Da fatan Allah ya hadamu da alkhairan cikinta, ya kuma tsaremu daga sharrin cikinta. Amin. Daga Aliyu Harazimi Ishak Fagge Kano 08068928028.
       
Edita ina fatan za ka isar min da sakon fatan alheri ga Kwamishinan Muhalli na Jihar Kaduna, Alhaji kasimu Lawal Awasco. Ya Allah Ka yi masa maganin ’yan tsurku. Daga Abdullahi Washa Muciya 08032933801

Ta’aziyya ga El-Rufa’i
Salam Aminiya ga sakon ta’aziyyata zuwa ga tsohon minister Malam Nasir el-Rufa’I na rasuwar kanensa. Allah Ya gafarta masa amin. Daga Idris Yaro Abuja 07061860202.

Ga Malam Shekarau
Aminiya ina so ku mika min sakona ga Malam Shekarau da zai koma PDP, to me jiya t ayi bare yau? Allah Ya raka taki gona. Daga Sani Muhammad Bichi 08075129644.

Jinjina ga Hon Rabi’u Idris Funtuwa
Jinjina kan dokar yaki da rashin da’a a kan luwadi da madigo da fyade. Daga Lawal Muhammad Hayin Ojo Zariya 08080796365.

Gan dan Majalisar karaye da Rogo
Ahmad Audi Zarewa ruwa ya kare wad an kada PDP da ANPP an hade, sai ka girbi abin d aka shuka. Hakan ai yayi. Daga Musa Abubakar Gajuna Rogo 08082272213.

Ga Malam shekarau
APC ta Jihar Kano ta rike tsintsiya da hannun hagu. Ina kira ga Malam Ibrahim Shekarau da magoya bayansa da ya kwashe ina ya zo ya tafi wata jam’iyyar, domin agololi sun share ‘’ya’yan masu gida. Domin kada Malam ya ja mana mutuwar almuru. Daga Tukur Maraya Shanono  08086560647.

Gwamna  Kwankwaso mai 100-100 a ilimi
Saboda nagarta da ka nuna wa ilmi kyauta tun daga firamari har zuwa jami’a,  ga shi an tura mutane sama da dubu biyu kasashen duniya don su karo karatu; ga mata guda 100 likitoci; ga masu zayyyanar gine-gine 100; ga matuka jirgin sama 100; ga masu tukin  jirgin ruwa; ga masu digiri na biyu sama da dubu daya; ga makarantun koyon sana’a 44; ga makarantar koyan larabci S.A.S 44; ga jami’o’i guda biyu. Mun gode, mun yaba. Allah ya ba ka Najeriya talaka ya ji dadi.
Daga Muhammadu Kano Kantin Kwari
08059718000

Kira ga kadiriyya
Aminiya ku taimaka ku ba mu dama ko fili a cikin wannan jarida don isar da sakon taya murna ga kadirawa, saboda zagayowar watan Maulidi, watan haihuwar Annabi Muhammad (SAW), a shekarar 1435. Daga Alhaji Kankat Jihar Gombe 07061316464.

Ga Baba Buhari
Baba Buhari gaskiya dokin karfe, kow aya gujeka sai ya dawo. Yau ga shi kai ne da gwamnoni 18.Muna taya ’yan majalisar tarayya ’yan PDP, wadanda suka koma APC murnan dawowa. Allah Ya taimake mu.  Daga Sani Abdu Beta 07068223015.

Gwamna Shema ya gyara ilimi
Edita don Allah ka fada wa diyan Dikko bincike ya nuna Gwamna Shema ya fi duk gwamnoni maida hankali ga ilimi. 2007 zuwa 2013 ya kashe sama da biliyan 100 kan gyara ilimi Firamare kadai. Gudun tangarda sai ya bada rikon Hukumar ga Dattijo Aminu danbaba. Shema mun gode. Allah Ya sa ka fi haka. Daga Amiru Isa Bakori 08075959086.

Gaisuwa ga kungiyar Gizago
Edita ina so a mika min gaisuwata ga kungiyar Gizago. Daga Aliyu Sani Sakkwato 0818918185516..

Ga ’yan jam’iyyar APC
Salam Aminiya ki ba ni dama in bayar da shawara ga duk dan jam’iyyar APC, a duk inda suke, su kasance masu hakuri; kada ku sake kwadayin shugabancin jam’iyya ko takara ya rusa hadin kanku. Da fatan Allah Ya kara mana zaman lafiya a kasarmu Najeriya da Duniya baki daya amin. Daga Bala Laba Mai Barcelona Garado Itas/Gadau, Jihar Bauchi 07032913391.