✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ga Hukumar Hisbata Kano

Salam, Edita zan yi amfani da wannan dama don na yi tambaya ga shugaban Hukumar Hisba, shin matar da ta nemi mijinta ya saketa shi…

Salam, Edita zan yi amfani da wannan dama don na yi tambaya ga shugaban Hukumar Hisba, shin matar da ta nemi mijinta ya saketa shi kuma me za ta ba shi? Ko kuwa hukuncin ya tsaya ne kawai a kan maza? Ko so ake a bai wa mata karfin cin zarafin mazajensu ne? Kun ga sun samu damar da za ta ci kwalar mijinta ta zagi iyayensa t ace ya saketa, idan ya isa. Akwai irin wadannan matan da yawa a cikin Kanon nan, ballantana idan ta san ba shi da dubu 50, kun ga an kwareshi, ba yarda zai yi. Na ji shugabar zawarawa na cewa dubu 250 ya kamata a ajiye idan za a saki ana kuma tunanin akai majalisa ta sa hannun zama doka. Wannan fa maganar ta abar duba wace. Daga Alhajin Dubai, Sardaunan Matasan Dala 07038605362.

Sakonnin waya

Wasikar Obasanjo
Editan Aminiya, ka ba ni dama domin bayyana ra’ayina kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba ni, akan  wasikar Obasanjo.  Addu’ar talakawan Najeriya  Allah (swt)  ya fara karba, domin fito da wadannan abubuwa da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya rubuta wa Jonathan, domin kuwa abu ne a zahiri karara. Kamar rashin tsaro da kabilanci da karya alkawari, domin yin takara a 2015, da yunkurin kashe mutane a kalla 1000 kafin zaben 2015. Daga Yakubu Yusuf Chiranchi, Kumbotso, Kano. 08036895095.

Taya murna ga daliban jami’o’i
Salam ina taya daliban jami’o’in kasar nan murana, bisa janye yajin aikin da malamansu suka yi.. Allah ya kiyaye gaba amin. Daga Bala Laba mai Barcelona Garado Itas/gadau, Jihar Bauchi 07032913391.

In ahakkokin malaman Katsina
Don Allah Aminiya ku tambayar mana shugaban Hukumar ilimin bai daya, ina hakkokin malaman Firamare suka makale? Misali in kana matakin albashi na 07/4 sai aka kai ka 08/2, amma babu kari, kai wasu ma ko kula su ba a yi. Daga Jibril 07060756068.

Ta’aziyyar Sheikh Harazimi
Innalillahi wa inna ilahir Raji’un. Bisa rasuwar ’yar uwata Sadiya Sunusi dantata da Malam Aliyu Harazumil. Allah Ya jikansu da rahama. Daga Aliyu Abbas Fagge. 07063957412.

Ta’aziyyar Shehu Aliyu Harazumi
Assalamu alaikum Aminiya ina so ki mika min ta’aziyya ga iyalan Shehu Aliyu Harazumi. Allah Ya jikansa. Allah ya gafarta masa. Daga Aliyu M. Faruk Gwagwalada Abuja. 07033983333.

Ta’aziyyar Sheikh Harazimi
Salam. Aminiya ina son ki mika ta’aziyyata ga duk dan darikar Tijjaniya a kan rashin fitaccen Shehun nan, wato Sheikh Aliyu Harazumi Hausawa Kano. Tijjanawa mun yi rashi Shehu. Domin Shehu yana daya daga cikin manya manyan shehun nan darikar Tijjaniya na Duniya gaba daya. Don haka muna rokon Allah da ya sanya mu hanya irin ta Shehu Barhama; sannan ya kaimu inda ya kai malamanmu na darikar Tijjaniya amin Daga Abdullahi Sanusi danja (Imamkhairi). 08092602127

Ina jin dadin labaranku
Assalamu alaikum, Aminiya da fatan kuna lafiya. Allah Yasa haka amin. Na yi wannan wasika ne domin in shaida muku ina matukar jin dadin labaranku. Kuma ina mika ta’aziyyata ga iyayen amarya A’isha da kuma mijinta. Daga Nasiru Muhammad Wafa Sakkwato 08031914141.

Wasikar Obasanjo
Wasikar Obasanjo ga Jonathan munafunci dodo ne me shi yakee ci. Kuma kira ga ‘’yan arewa kar su yarda da wannan keken beran. Daga 08092533100.

Hattara PDP
A Jihar Sakkwato ba wata jam’iyya in ba APC ba, inma akwaita to gawa ce. Bafarawa ya kashe jam’iyayr PDP kuma ta zamo gawa. Ni Musty shaida ne Sakkwatawa muna godiya. Daga Musty Sok. 08034068363.

Kwankwaso ka sanya takalmin karfe
Edita ina kira ga tauraron gwamnoni Najeriya, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso cewA: gyaran masallatan Juma’a guda 44 da ke Jihar Kano da sauran  rina a kaba. Kwankwaso ka kai ziyarar ba zata a wasu masallatan za ka ga abin kunya da ’yan kwmaitin gyaran suka tafka. Sun ci amanar Musulunci, sun ci amanar gwamna. Daga Ali Fancy Garko a Kano. 08171748500.

Godiya ga Kwankwaso
Muna godiya ga Gwmanan Jihar Kano, Injiniya Kwankwaso da dimbin ayyukan alheri d ayake gudanarwa a cikin Jihar Kano da kewaye. Ya zama wajibi mu yi godiya ga gwamnan gwamnoni masu yin talakawa gwamna mai tausayi. Allah Ya ja kwana, Ya kara lafiya. Daga AbdulHamid Abubakar Yaro Kano. 08069805518.

Ga Edita
Don Allah Edita ko kuna da wani sharadi da ake bi kafin a buga wa mutum sakon da ya aiko ga wannan jarida, wato Aminiya. Domin na yi aike har na gaji, ina bata wa kaina lokaci. Idan kudi ake biya a taimaka a fada min yadda zan aiko. A bugo min. Daga Malam Adamu Mamman, Gwadabawa, Jihar Sakkwato 07066018903.

PDP talakawa sun gane
Idan tururuwa ta soma lallacewa fuka-fukai take yi. PDP mu dai talakawa mun gnao irin zaluncinku. Allah Ya kaimu 2015. Daga Usman Bala 07037084451.

Ga Shugaban karamar Hukumar Miga
Assalamu alaikum,. Don Alah Editan wannan jarida mai albarka ta Aminiya ina son sanar da Shugaban karamar Hukumar Miga, Muhamamd Sabi’u Miga da ya janye kudurinsa na neman zarewa, domin talauci ya yi wa al’umma yawa. Bana sai mun yi cabnji,. Mun dauko dan kwarai. Daga Baba Habu Miga 08038932782.

Koma bayan ilimi a Sakkwato
Edita ina so ka mika min sakona ga shugaban makarantar AbdurRasheed Adisa Raji, wadda aka fi sani da  Raji a Sakkwato, da ya cire son rai ga harkar ilimi a makaranta.. Saboda haka ne koma bayan ilimi a Sakkwato Daga Aliyu Aliyu 08107077591.

Ga Aminiya
Assalamu alaikum jarida mai taimaka wa wajen wayar da kan jama’a musamman gama su nauyin fahimta wadanda za su tsaya da gaske, akan al’amari ba haka yake ba, amma da zarar an nuna wa mutum abu kuma an karanta masa da yarensa sai ka ga ya saki koda ba Hausa ba ce yarensa. Daga Muhammad Minjibir, mazaunin Benin. 08131812118.

Ga Edita
Asssalam. Nagode Edita da irin kokarin da kuke yi na buga wa mutane sakonninsu. Allah Ya kara basira Edita, amin. Daga M.D. Sani Bararo, Hausawa, Kano 08038492252.