Akalla Fulani dubu uku da tara ne rikicin kabilanci a Kudancin Kaduna ya tilasta wa gudun hijira, inda suke cikin mawuyacin hali a sansanonin ‘yan gudun hijira.
Shugabannin Gamayyar Kungiyoyin Fulani Makiyaya sun nuna kaduwa da abin da suka kira goyon bayan Kungiyar Mutanen Kudancin Kaduna (SOKAPU) ga harin da aka kashe Fulani, wasu suka bace, aka kuma kona dukiyoyinsu a yankunan Zangon Kataf da Kauru.
- Kaduna ta fadada dokar kullen Zangon Kataf da Kauru
- ‘Yan bindiga sun kashe mutum 9 a Kaduna
- Yadda rayuwar masu gyaran citta ke gudana a Kudancin Kaduna
“Ya kamata SOKAPU ta yi bayani ga wadanda abin ya shafa dalilin yi wa masu zanga-zangar lumana kan rikicin iyaka irin wannan danyen aikin”, inji jawabinsu ga ‘yan jarida.
Shugabannin kungiyoyin sun bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su yi watsi da abin da suka kira bi-ta-da-kullin SOKAPU da mukarrabanta, ta hanyar kara azama wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan.
Shugabannin Fulanin da suka hada da Alhaji HarunaTugga, Ardo Idris Gundaru, Barista Nuhu Ibrahm, Abbas J. Julde da Barista Abubakar Ibrahim Naseh, sun ce:
“Mun yi mamakin jawabin Kakakin SOKAPU na 30 ga watan Yuni, 2020, da ke goyon bayan kashe-kashe da kone-konen da matasan Atyap da na Tsam a Kananan Hukumomin Zankon Kataf da Kaura suka yi wa Fulani 99, wasu 139 suka bace, aka kuma kona gidaje 290 bayan sace-sacen da aka yi musu.
Sun yi zargin cewa, “Matasan Atyap da suka yi kone-konen sun kashe dabbobi 429, wasu 4,009 sun bace ko an sace, bisa kiyasnin binciken da aka yi zuwa ranar 17 ga watan Yuni, 2020”.
Fulani sun yi watsi da zargin SOKAPU
Sun kuma yi watsi da zargin SOKAPU cewa gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar kulle a yankunan ne sakamakon jawabinsu na ranar 17 ga watan Yuni mai ‘cike da batanci da tunzuri’.
“Sanin kowa ne cewa Gwamantin Jihar ta sanya dokar ranar 11 ga watan Yuni ne bayan kazamin harin da ‘yan SOKAPU suka kai wa iyalan Fulani makiyaya”, inji su.
Sanarwar ta ce zuwa yanzu karin wasu Fulani biyu sun rasu, an gano 1,067 daga cikin shanun da suka bace, wasu 19 kuma an kashe su, baya ga awaki da tumaki.
“Sun san wasu sarakuna da shugabannin al’umma da suka taimaka, kuma muna da kwarin gwiwa game da hukumomin tare bayanan sirri. Muna kira da a tsare su a gurfanar da su”, inji su.
Rikicin kudancin Kaduna ya kazance a baya-bayan nan musamman biyo bayan rikici kan filayen gona, wanda sakamakonsa gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita na sa’a 24 a kananan hukumomin biyu.