✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Francisca ta yi nadamar yi wa kungiyar Super Falcons kwallo

’Yar kwallon kungiyar Super Falcons ta Najeriya da ke zaune a Amurka Francisca Ordega ta ce ta yi nadamar buga wa kungiyar kwallon kafa ta…

’Yar kwallon kungiyar Super Falcons ta Najeriya da ke zaune a Amurka Francisca Ordega ta ce ta yi nadamar buga wa kungiyar kwallon kafa ta Super Falcons kwallo ganin yadda ake yi wa ’yan kwallon matan Najeriya rikon sakainar kashi.

A wata hira da ta yi kafar watsa labarin wasanni na Africanfootball.com a ranar Talatar da ta wuce ta ce, da alama gwamnatin Najeriya ba da gaske take yi wajen karfafawa matan Najeriya gwiwa a harkar kwallo ba. Ta ce baya ga yi wa Najeriya kwallo a mataki daban-daban kuma har yanzu ba ta ga wani canji mai ma’ana ba ya sa ta yi wannan nadama.
’Yar kwallon dai ta taba buga wa kungiyar kwallon kafa ta mata ta ’yan kasa da shekara 17 da ta ’yan kasa da shekara 20 kafin ta yi wa Super Falcons kwallo, ta ce da ba ta buga wa Super Falcons kwallo ba, da ta koma wata kasa don cigaba da yin wasan kwallo.
Ta ce idan gwamnatin tarayya ba ta dauki mataki ba, to nan gaba da wuya a samu matan da za su cigaba da yi wa Najeriya kwallo.
Wadannan kalamai na ’yar kwallon ba za su rasa nasaba da yadda Hukumar NFF ta nuna musu rashin kula tun bayan da suka lashe kofin Afirka na mata a ranar Lahadin da ta wuce Kamaru ba.
’Yar kwallon tana daga cikin ’yan kwallon da suka samun asarar lashe kofuna uku daga cikin 10 da Falcons ta lashe a baya.