Kungiyar Mata Musulmai ta Najeriya (FOMWAN) ta bayyana kaduwar ta da rasuwar shahararren malamin addinin Musuluncin nan, Sheik Ahamd Lemu.
Shugabar kwamitin watsa labarai da dab’i ta kungiyar, Hajia Bilqees Oladimeji ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Ilorin babban birnin jihar Kwara ranar Alhamis, tana mai bayyana malamin a matsayin wani ginshiki kuma abin koyi.
- Muryar Sheikh Ahmed Lemu ta kara fito da hasken addinin Islama —Buhari
- Tarihi da rayuwar Sheikh Ahmed Lemu (1929-2020)
Sheik Lemu, fitaccen malamin addinin Musulunci kuma tsohon babban alkalin kotun sharia’r Musulunci dai ya rasu ne ranar Alhamis a garin Minna na jihar Neja yana da shekaru 91 a duniya.
Sanarwar, ta rawaito shugabar kungiyar ta kasa, Hajiya Halima Jubril na bayyana cewa shehin malamin ya taimaka matuka wajen yada Musulunci a Najeriya.
“A cikin shekarun 1970, lokacin da makarantun Kiristoci ba za su iya koya darussan Musulunci ba a makarantun su, Sheik Lemu da ’yan tawagar sa ba tare da bata lokaci ba suka debo malamai tare da tura su makarantun domin koyar da darussan,” inji ta.
Ta ce malamin ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen samun ilimin mata da dama wanda hakan ya taimaka musu matuka wajen ci gaban su.
“Mu a FOMWAN, Sheik Lemu wani ginshiki ne, malami kuma uba wanda ya karfafa mana gwiwa har muka kai ga nasara.
“A karkashin koyarwar sa, mambobin mu sun koyi ilimin Kur’ani da Hadisi tare da yin amfani da su a rayuwar su.
“Ya bayar da gudunmawa sosai wajen kwato hakkin mata kamar yadda Allah ya ce a ba su,” inji ta.