An gano wani Firinji mafi tsufa a Birtaniya da ke ci gaba da aiki bayan shekara 80.
Firinjin wanda aka kera a 1930, inda wadansu iyalai suka mallake shi bayan sun saye shi a 1949 kuma suke fata ’ya’ya da jikoki su gaje shi daga gare su.
- Majalisa ta gindaya sharudan kirkirar sabbin jihohi
- Ana Laluben Hanyar Sa Yara Miliyan 10 A Makaranta A Najeriya
Mamallakin firijin wanda aka bayyana sunansa da Robert mai shekara 81, tsohon ma’aikacin jiragen kasa ne, ya ce firinjin yana da fadin kafa biyu da tsawon kafa uku kuma yana ajiye ne a garejin gidansu.
Ya ce har yanzu firinjin yana aiki kuma ya kamata “A ba shi lambar yabo ta zinare kan dadewa yana aiki.”
A makon jiya tilas ta sa Robert da matarsa dogaro da tsohon firinjin bayan da firinjinsu na zamani ya lalace sakamakon tsananin zafin da ake fama da shi a kasar Ingila.
Wani mai sayar da firinji mai suna Jonathan Kerry ya sha mamaki lokacin da ya ga tsohon firinjin bayan da iyalan suka kira shi don ya gyara musu sabon firinjinsu da ya lalace.
Robert ya ce “Bakon abu ne ka mallaki firinji a wadancan shekarun, saboda “A lokacin har kwatance ake yi da mu cewa mun mallaki firinji.”
Iyayen matar ce suka saya wa ma’auratan firinjin, inda suka dauke shi zuwa birnin Sussed, wurin da suka zauna na tsawon shekara 40 kafin su koma garin Gloucestershire a shekarar 2006.
Robert ya kara da cewa: “Wannan gado ne na iyalai. Muna fata mu gadar da shi ga na bayanmu.”
Ya shaida wa jaridar Daily Mirror cewa, firinjin “wani jakin aiki ne. Hakika ya cancanci lambar yabo ta dadewa yana aiki.
Mukan yi amfani da shi a lokutan Kirsimeti, lokacin da muke bukatar karin fili ko wurin adana kayan marmari da bazara. Yana aiki sosai.
Muna matukar farin cikin ci gaba da kula da shi zuwa wasu shekaru masu zuwa.”
Wani jami’i a yankin ya ce, “Iyayensu sun sayi firinjin ne na hannu a kan Fam 49 a 1949. Suna ma da rasit din sayen. Yana garejinsu kuma yana aiki”