✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Firimiyar Najeriya: Nasarawa United ta tunkudo Pillars daga mataki na biyu

Nasarawa United ta yi kankan da maki 55 tare da Pillars.

Nasarawa United ta koma mataki na biyu a teburin gasar Firimiyar Najeriya bayan ta lallasa Jigawa Golden Stars da ci 3-1 wadda ta kai mata ziyara a ranar Litinin.

Wasan wanda shi ne na mako na 31 da aka dage zuwa jiya, Nasarawa United ta samu damar haurowa daga mataki na hudu zuwa na biyu a teburin sakamakon nasarar da ta samu a filin wasa na Lafia Township.

Rahotanni sun ce tun a mintunan farko na wasan ne Nasarawa United ta nuna bajinta wanda hakan ya kai ga kungiyar ta kusa jefa kwallo ta farko a ragar ’yan wasan da suka zo daga garin Hadejia.

Sai dai dan wasan Silas Nwakwo ya yi kullewar kai inda ya zubar da damarsa duk da ya kasance daga shi sai mai tsaron ragar abokiyar karawar ta su a tazarar da bata wuce matakin bugun fenareti ba.

Sai dai ya wanke kuskuren da ya yi na buga kwallon da ya yi ta baude, inda a minti na 19 ya sakada kwallo ta farko da kungiyarsa ta ci.

Haka kuma, a minti na 31 na Nwakwo ya sake jefa kwallo ta biyu a wasan, inda a yanzu kwallayen da ya ci a gasar suka zama 13 kenan yayin da zamanto dan wasa mafi zira kwallaye a kakar Firimiyar Najeriya ta bana.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, Nwakwo ya yi amfani da damarsa wajen kwallo ta biyu yayin wata zari-zuga da kungiyarsa ta yi a wasan.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne Nasarawa United ta jefa kwallo ta uku ta hannu dan wasanta Adamu Hassan, bayan Aliyu Adamu ya ajiye masa wata kwallo mai kyawun gaske a minti na 59 a cikin zagayen bugun fenareti.

Jigawa Golden Stars ta rage yawan kwallayen ta hannu Samuel Stone, wanda ya ci mata kwallon daya tilo a wasan a wani bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Da yake zanta wa da manema labarai bayan an tashi wasan, Kocin Nasarawa United, Bala Nikyu, ya yaba wa kokarin da ’yan wasan suka yi, lamarin da ya alakanta da kyakkyawan shirin da suka yi gabanin wasan.

Nasarawa United ta tunkudo Pillars daga mataki na biyu

Aminiya ta ruwaito cewa, bayan wannan sakamako, Nasarawa United ta tunkudo Kano Pillars daga mataki na biyu a gasar, wacce ta yi daraf tun a ranar Lahadi.

Nasarawa United ta koma ta biyu sakamakon yawan kwallaye duk da ta yi kankan da maki 55 tare da Pillars.

A ranar Litinin ce bayan buga wasanni mako na 31, kungiyar Akwa United ta ci gaba da jan ragama a teburin gasar Firimiyar Najeriya.

Har yanzu Akwa United tana saman teburin da maki 57, bayan ta buga wasanta na ranar babu ci a gidan Plateau United.

Kano Pillars da ke mataki na biyu a yanzu wacce a wasu makonni baya ta rika ’yar bani-in-baka a zaman saman teburin, ta hada maki 55 a mako na 31 na gasar.

Pillars wacce ake yi wa lakabi da sai masu gida ta samu nasarar samun maki uku yayin da lallasa Lobi Stars da ci 3-0 a karawar da suka yi a Jihar  Kaduna.