✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Firimiyar Ingila: Jibi Man United za ta hadu da Man City

A ci gaba da gasar rukunin firimiyar Ingila, a jibi Lahadi idan Allah Ya kaimu ake sa ran za a yi wasa mai zafi a…

A ci gaba da gasar rukunin firimiyar Ingila, a jibi Lahadi idan Allah Ya kaimu ake sa ran za a yi wasa mai zafi a tsakanin manyan kungiyoyin da ke buga gasar.  Manchester United ce za ta karbi bakuncin kulob din Manchester City a wasan da ake ganin zai fi kowane wasa zafi.

Kawo yanzu Manchester City ce take saman teburin gasar da maki 43 a wasanni 15 yayin da Manchester United ke matsayi na biyu da maki 35 a wasanni 15.

Wani abin sha’awa shi ne har yanzu kulob din Manchester City ce kadai ba ta samu rashin nasara a gasar ba, inda ta samu nasara a wasanni 14 yayin da ta yi kunnen doki a wasa daya kacal.  Don haka kocin City Pep Guardiola zai yi duk mai yiwuwa ya samu nasara a kan United don ya kafa sabon tarihi kamar yadda kocin United Jose Mourinho zai yi duk mai yiwuwa ya ga ya samu nasara a kan City.

Ana sa ran gidajen kallon kwallo za su cika makil da magoya baya don ganin yadda wannan wasa zai kaya, inda tuni aka fara muhawara.  Yayin da wasu ke ganin City ce za ta lallasa United a wasan, wasu kuwa gani su ke United ba kanwar lasa ba ce hasalima ita ce za ta karya lagon City wajen doke kulob din a karon farko a gasar ta bana.