Firaministan Bahrain, Khalifa Bin Salman Al Khalifa, ya rasu bayan shafe shekaru 49 a kan mulki.
Khalifa, wanda ya fara mulkin kasar tun shekarar 1971 ya rasu yana da shekaru 84 a duniya, kamar yadda Babbar Kotun kasar ta sanar a ranar Laraba.
- Ya yi yunkurin shiga Saudiyya da kwalaben giya cikin aljihu
- Jerin kasashe da Saudiyya ta gindaya wa sharadin shiga cikinta
Kamfanin Dillacin Labarai na BNA ya rawaito cewa firaministan ya rasu ne a Asibitin Mayo dake jihar Minnesota ta Amurka.
Tuni dai Sarkin kasar ta Bahrain, Hamad bin Isa bin Salman ya mika sakon ta’aziyyarsa kan rasuwar tsohon firaministan
Ana sa ran gudanar da jana’izarsa da zarar gawarsa ta isa kasar, ko da dai ance ‘yan tsiraru daga cikin iyalansa ne kawai za a bari su halarta.
Sarkin kasar ya ba da umarnin a sauke tutocin kasar kasa-kasa yayin da ma’aikatu da hukumomin gwamnati za su kasance a rufe na tsawon kwanaki uku domin nuna alhini da rasuwar tasa.