✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Finidi George ya amince ya horar da Golden Eaglets kyauta

Tsohon dan kwallon Super Eagles Finidi George ya amince ya horar da kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 (U-17) idan aka ba…

Tsohon dan kwallon Super Eagles Finidi George ya amince ya horar da kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 (U-17) idan aka ba shi dama ba tare da ya karbi ko sisin kwabo ba kamar yadda rahotanni suka nuna.

Finidi yana daya daga cikin mutum 59 da Hukumar Shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta gayyata don ganawa da su a kan yiwuwar zabar daya daga cikinsu don ya zama kocin kungiyar.

Kamar yadda kafar watsa labaran wasanni ta SCORENigeria ta tabbatar ta ce kocin ya shaida mata cewa idan aka ba shi dama, zai iya horar da kungiyar ba tare da ana biyansa albashi ba, saboda ya lura Hukumar NFF tana fama da karancin kudi, kuma abin da ya sa kenan yake son ya bayar da tasa gudunmawa wajen farfado da harkar kwallon kafa a kasar nan.

“Na amince na horar da kungiyar U-17 kyauta idan aka ba ni dama, saboda na lura NFF tana fama da karancin kudi,” inji shi.

Finidi George dai ya taba yin kwallo tare da tsohon kocin U-17 Emmanuel Amunike a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da hakan ta sa ake ganin akwai yiwuwar NFF ta ba shi dama wajen horar da kungiyar U-17.