✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fim din Black Panther ya samu sama da Dala biliyan daya a cikin wata daya

Fim din ke tashe a ’yan kwanakin nan a duniya, Black Panther ya samar da makudan kudi har sama da Dalar Amurka biliyan daya a…

Fim din ke tashe a ’yan kwanakin nan a duniya, Black Panther ya samar da makudan kudi har sama da Dalar Amurka biliyan daya a cikin wata daya.

Wannan fim din dai har yanzu a silima kawai ake haska shi, amma abin mamaki yana samu wannan tagomashi. 

Yanzu Black Panther ne fim na biyar da ya samu wannan tagomashi a tarihin duniya, sauran su ne a kamfanin shirya fim na Marbel. Baya ga fim din Black Panther, wasu fina-finan  da suka samu wannan tagomashi sun hada da The Abengers da Iron Man 3 da Age of Ultron da Cibil War da Captain America. Sannan Black Panther ne ya zamo na farko da ya samu wannan matsayi a shekarar 2018. 

Fim din yana nuni ne a kan tarihin Afirka, inda aka yi labarin yadda wani jarumi ya tauna wani magani ya samu wani irin asiri mai karfi mai suna bibranium wanda kabilu biyar suke fada a kai, kuma hakan ya sanya ya zama Black Panther na farko. Sai ya hada dukan kabilun gari amma ban da Jabari domin kafa daular Wakanda. Sai su mutaenn daular Wakanda suka ware kansu suka koma gefe suna ambaton kansu a matsayin duniya ta daban.

Daga baya sai rigima ta barke a tsakanin Sarki T’Chaka da dan uwansa N’Jobu wanda yake zargi da taimakon wani mai safarar makamai Ulysses Klaue wajen satar asirinsu na bibranium daga Wakanda.  

Bayan rasuwar T’Chaka, sai dansa T’Challa ya koma Wakanda ya zama sabon Sarki. Da shi da Shugaban Rundunar Dora Milijaje Okoye  suka shirya yadda tsohuwar budurwarsa za ta halarci taron rantsar da shi tare da mahaifiyarsa Ramonda da kanwarsa Shuri. A wajen bikin nada shi, sai shugaban kabilar Jabari M’Baku ya kalubalanci zamansa Sarki ta hanyar amfani da bakaken asiri, inda T’Challa ya samu nasarar doke shi a asiri mafi karfi.

Shirin dai a takaice yana nuni ne a kan sarauta da yadda kasashen Afirka suke ci gaba da ilimi tun a zamanin da.