✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

FIFA ta karrama tsohon golan Najeriya bincent Enyeama

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles bincent Enyeama ya samu kyauta daga hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) saboda namijin kokarin da…

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles bincent Enyeama ya samu kyauta daga hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) saboda namijin kokarin da yake yi a gasar rukunin Faransa da aka fi sani da Ligue 1.
Tsohon golan Najeriya Enyeama wanda ya fi kowane dan kwallon Super Eagles yi wa kungiyar kwallo, kawo yanzu ya buga wasanni fiye da 100 ga kungiyar kwallon kafa ta Lille.
dan kwallon ya bayyana kyautar da ya samu ne a kafar watsa labaransa na Instagram in da aka gan shi dauke da kofi inda ya sanar da masoyansa halin da yake ciki a ranar Litinin da ta gabata. “Hukumar FIFA ta ba ni kyauta saboda kokari da kuma kwazon da nake nunawa a kulob din Lille, don haka ina yi wa duk wanda ya karanta wannan bayani nawa fatan alheri musamman a wannan wata na Maris, 2016.
Hukumar FIFA ta karrama Enyeama ne a matsayin bakin fata da ya fito daga yankin Afirka wanda yake kokari a gasar rukunin Faransa.
Enyeama, dan kimanin shekara 33 ya yi ritaya daga yi wa kungiyar Super Eagles kwallo ne tun bayan ya samu sabani da tsohon kocin kungiyar Sunday Oliseh.
Jim kadan bayan Oliseh ya ajiye aiki a makon jiya ne sai aka rika rade-radin Enyeama zai sake komawa kungiyar, amma dan kwallon ya musanta hakan, inda ya ce a kai kasuwa.