Edita don Allah ka ba ni dama in yi tsokaci dangane da ficewar tsohon Shugaban Najeriya, wato Obasanjo daga PDP. Hakika ficewar tasa ba ta zo mana da mamaki ba, ganin yadda aka dade ana zaman doya da manja, tsakanin Shugaba Jonatan da Obasanjo, tabbas PDP ta dade tana gallaza wa talakawan kasar nan, musamman wajen kama karya da ta dade tana yi. To yau dai ta faru, ta kare, shugaban dattawa shi ma ya tattara kayansa, ya kara gaba. Abin tambaya, ko ficewar tasa za ta zame wa shugabannin jam’iyyar darasi? Daga Aminu Abdu Baka Noma, Sani Mainagge, Kano 08099479880.
Kira ga talakawa
Lallai talakawa ku kare mutuncinku. Abin bakin ciki ma wai sai kun bada katin zaben ko an juyi lambar jikinsa, wato “copy serial number,” kafin a ba ku taki buhu daya. Wannan abin kunya har yaushe. Daga Mahmoud Muhammed Dambazau, Jos.
Magajin Shema
Edita Allah ya saka da alheri. Hakika Edita kai ne Magajin Sardauna na asali, amma don Allah ka ba ni fili in yi godiya ga Gwamna Shema mai albarka. Sannan ka ba ni fili in tunatar da jama’ar Jihar Katsina masu albarka, kan mu zabi Musa Nashuni Ikon Allah da Gambo Rabi’u bawan Allah; Dattijo Abdullahi Faskari da Ajiya Ibrahim Tukur. Don su ne kadai za su ci gaba da ayyukan alherin da Baba Nashema mai albarka ke yi. Daga Amiru Isa Bakori, 07068147933.
Ko na yi wa Aminiya laifi?
Assalamu alaikum. Editan.Aminiya wai ko na yi laifi ne ba ka son buga sakona. Ai ya kamata a matsayina na mai tallar Aminiya a Apapa Legas, ni ma a sani. Kowane mako sai na turo da sako, amma a banza. Da fatan za a yafe min. Daga Yahaya Ahmed Jabo, Apapa Lagos 08026392800.
Mu zabi cancanta
Assalamu alaikum al’ummar Jihar Kano, mu zabi cancanta, babu zancen APC sak. Mu dai zabi Buhari kawai, Gwamna kuwa sai mu yi gini iya linta. Da fatan Kanawa sun gane. Daga Abdulrashid Loi dandago. 08116514183.
Mu yi addu’a ga kasa
Salam ya ’yan uwana talakawan Najeriya, mu tashi da addu’a, domin yanzu sai mun tashi tsaye, Allah Ya kawo mana mafita daga daukacin matsalolin da suka baibaye al’ummar kasar nan. Daga Salisu Maliya Goron-Dutse, Jihar Kano 08099139741.
Shekau dan PDP ne
Salam. Aminiya ku gaya wa Abubakar Shekau an yi walkiya mun gan ka, kai dan PDP ne, ba dan Boko Haram ba. Daga Muhammad Sirajo Hamidu, bictoria Island, Jihar Legas.
A dubi matasa
Edita ka ba ni dama in yi tsokaci dangane da rashin ayukkan yi, da ya yi wa matasa kaka gida a sassa daban-daban na kasar mu Najeriya. Wannan ba karamin tasiri ya yi ba, wajen jefa dimbin matasa cikin mawuyacin halin rayuwa, wanda ke kai su fadawa shan kayan maye da aikata fasadi. Saboda haka wannan babban kalubale ne, ga gwamnatocin jihohi, da gwamnatin tarayya, da ma ‘yan kasuwa, don su tashi tsaye, wajen samar wa matasa da ayyukan yi da kuma kafa masana’antu, domin amfanin matasa da zai rage zaman kashe wando. Daga Aminu Dankaduna Amanawa.
09035522212.
Addu’a ga Aminiya
Gaisuwa ga Aminiya, ni mai karanta Aminiya ne Allah Ya kare ku. Daga Mista Malta Dickau a Maiduguri 07038655371.
Jega ka yi gaskiya
Salam. Don Allah Jega ka kamanta gaskiya ga zabe mai zuwa. Allah Ya taimake ka wajen aiwatar da gaskiya. Daga Kamilu Hamcheta Mani Katsina 08143436759.
Kira ga mata
Edita ka isar da kirana ga iyaye mata kan yadda fyade ya yawaita ga kananan yara. Domin mutanen da ke aikata masha’a da fyade ga kananan yara su ke dada hargitsa kasar nan, inda musifu ke dada karuwa. Hakika gwamnati ta ki daukar mataki. Mu tashi mu zabi shugaba nagari. Mu dage da addu’a; Allah Ya kawo mana mafita, Ya kare mutuncinmu da ’ya’yanmu. Daga Hajiya Salma Saeed Jos. 08032409873
Ta’aziyya ga al’umma
Edita ka isar da sakon ta’aziyyata ga ’yan uwna wadanda harin bom ya rutsa da su a jihohin Gombe da Bauchi da Kano. Wadanda suka rasu Allah Ya jikansu, ya sa aljanna ce makomarsu. Mu da muka rage Allah Yak are mu. Daga Aisha M. Ali Polo Sakkwato 08064799127.
Mu yaki sauro
Edita. Hadisi ya rigaya tsafta bangare ne na imani. Don haka mu jajirce wajen yaki da suaro, domin cutar zazzbin maleriya na kassara rayuwarmu. Mutanen Arewa da ke zaune a yankuna masu zafi lallai mu tsaftace muhalli, mu gyara magudanan ruwa, don gudun illar cutar sauro. Daga Bilya Daura 08132511159.
Kira ga Masari
Editan Aminiya ka ba ni dama in yi kira ga Alhaji Aminu Bello Masari da ya hada kai da suaran ’yan takarar jam’iyyarsa, ta yadda za a kai ga nasara. Allah Ya ba shi ikon yin adalci a tsakanin al’ummar Jihar Katsina. Mun tunkari PDP. Allah Ya bai wa APC nasara a kowane mataki, tun daga kansila zuwa Shugaban kasa. Amin. Daga Alhaji Babangida A. Malumfashi 08063169007.
Kira ga Tata
Editan Aminiya don girman Allah ka isar min da sakona Umar Abdullahi Tsauri, wato Tata. Allah Ya ba ka Gwamnan Jihar Katsina. Amin. Daga Maman Ihsan Ibadan 08035793428.
Shettima ya fi Sherrif
Edita Gwamna Kashim Shettima ya fi Sherrif da ’yan korensa, irimn su Muhammad Wakil. Kuma kun yi sake dan Zaki ya girma. Allah Ya kara taimakon Gwamna Shettima ya ci gaba da ayyukan kwarai. Mu kuma dage da addu’ar neman mafita daga matsanancin halin tsaro da yankinmu ke fama da shi. Daga Aliyu Sani Biu Maiduguri 08055984868.
Addu’ar neman mafita
Edita, yanzu dai tashin bom ya zama ba sabo ba a karamar Hukumata ta Potiskum da kuma Jihata ta Yobe, da ma fadin yankin mu na Arewa. Shin a haka za mu ci gaba da rayuwa? Kullum mutum ba zai ji labari mai dadi ba, sai na bakin ciki. Ya Allah muna rokonka da ka kawo mana tabbatacciyar mafita a wannan rayuwa. Masu mummunar aniya akan mu, Allah ka mayar musu. Amin Summa Amin. Daga Usman bn Affan Damaturu.