Sauyin sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC da tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya yi, ta haifar da tababa a tsakanin al’ummar mazabarsa ta Dass da Tafawa Balewa da Bogoro a Jihar Bauchi.
Wata kungiyar siyasa mai ikirarin kishin al’ummar Bogoro, Dass da Tafawa Balewa, ta zargi Dogara da cin amana gami da yaudara a sauyin shekar da ya yi ba tare da tuntubar mazabarsa ba.
Da yake ganawa da manema labarai, shugaban kungiyar, Mista Sama’ila Shekarau, ya ce akidar son zuciya ce ta sanya Dogara ya sauya sheka ba tare da neman shawarar al’ummar mazabar da ya ke wakilci a tarayya ba.
Shekarau ya tafi a kan cewa Dogara bai tuntubesu gabanin komawa jam’iyyar APC, lamarin da ya ce manuniya ce ta rashin daukar mazabarsa da muhimmanci kuma ba a bakin komai ba.
Kungiyar na zargin Dogara da kin halartar zaman Majalisar Tarayya, saboda haka a cewarsu, mazabarsu ta koma baya wajen tafiyar da harkokin kasa.
Ta sake jaddada goyon bayanta a kan jagorancin Gwamna Bala Muhammad da kuma jam’iyyar PDP.
– ‘Muna tare da Dogara a APC’
Haka kuma wata kungiyar matasa magoya bayan ci gaban Kananan Hukumomin Tafawa Balewa, Dass, da Bogoro (TDBYDF), ta bayyana goyon bayanta ga matakin Dogara na sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Kungiyar tana mai cewa, Dogara shi ne turbar siyasa da suka yada zangonsu a kai kuma ba su da niyyar sauka.
Da yake bayyana ra’ayin, shugaban kungiyar, Injiniya Emmanuel Isheni, ya ce Jihar Bauchi ta sauka daga tubalin da aka san ta a kai, na kwarewa a fagen siyasa, da kuma zaman lafiya tsawon shekaru aru-aru sakamakon rikon sakainar kashi da Gwamna Bala Muhammad yake yi wa akalar jagorancin jihar.
Kungiyar ta ce tsarin jagoranci da Gwamnan ya dauko bai dauki talakawa da matasan jihar a bakin komai ba.
– Kwamishina ya jefar da Gwamna ya bi Dogara
A bangare guda kuma Kwamishinan Masana’antu da Kasuwanci na Jihar Bauchi, Muhammadu Alhassan Sadiq, ya yi murabus daga mukaminsa.
Honarabul Sadiq ya ya ce sauka daga kujerar da ya yi na da babbar nasaba da sauyin shekar Dogara daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Ya ce: “Duk abin da ya yi farko yana da karshe, a yau 19 ga watan Agustan 2020, na yi murabus daga mukamin Kwamishinan Masana’antu da Kasuwanci na Jihar Bauchi”.
Aminiya ta fahimci cewa, Honarabul Sadiq ya kasance daya daga cikin ‘yan gani-kashe-nin Dogara, wanda a baya-bayan nan ya shiga rudani a sakamakon takun sakar da ke tsakanin ubangidan nasa da kuma Gwamna Bala Muhammad.