Fitacciyar jaruma Fati Ladan ta yi bankwana da masana’antar shirya fina-finan Hausa bayan an daura mata aure a ranar Juma’a 20 ga watan Disamba, 2013.
Jarumar ta bayyana wa wakilinmu cewa burinta ya cika kuma ta yi farin ciki da ta rabu da kowa lafiya, sannan ta yi wa sauran jarumai mata addu’ar gamawa da masana’antar lafiya.
Ta ce: “A yanzu burina ya cika kuma ina cikin farin ciki domin na rabu da kowa lafiya. Ga sauran jarumai mata ina yi musu addu’ar gamawa da masana’antar lafiya. Duk wanda ya yi mini laifi na yafe masa, don haka zan yi amfani da wannan damar don na roki gafarar duk wanda na batawa.”
An daura auren Fati Ladan da Alhaji Usman Yarima Shettima a gidan mahaifan jarumar da ke Titin Saulawa a Unguwar Sarkin Musulmi da ke Kaduna bayan Sallar Juma’a a kan sadaki Naira dubu 150.
A cikin wadanda suka halarci daurin auren akwai tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa da Manjo Hamza El-Mustapha da Kwamared Shehu Sani da sauransu.
An gudanar da dina a otal din Royal Tropicana da ke Titin Isah Kaita a Kaduna. A lokacin da babban bako Manjo Hamza Al-Mustapha yake jawabi ne ya yaba wa kishiyar Fati Ladan sakamakon yadda ta caba kwalliya ta kuma nuna farin cikinta, inda ya ce sai an tace ake samun mace kamar kishiyar Fati.
Amarya ta tare a gidan mijinta da ke Ibiteye da ke Kabala kusa da masallacin Al-Mannar da ke Kaduna.
A cikin ‘yan fim da suka halarci dinar akwai Ali Nuhu da Sadik Sani Sadik da Rasheeda Adamu Abdullahi da Abida Muhammad da Hadiza Gabon da Fadila Muhammad da Rahama Sadau da sauransu.
Fati Ladan ta yi bankwana da Kannywood
Fitacciyar jaruma Fati Ladan ta yi bankwana da masana’antar shirya fina-finan Hausa bayan an daura mata aure a ranar Juma’a 20 ga watan Disamba, 2013.Jarumar…
