✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fatanmu a gudanar da zabe lafiya

Edita, ina mika sakon gaisuwata ga dukkan al’ummar Najeriya. Ina taya su murnar zagayowar sabuwar shekarar ’yan albashi ta 2015. Allah Ya sa mu ga…

Edita, ina mika sakon gaisuwata ga dukkan al’ummar Najeriya. Ina taya su murnar zagayowar sabuwar shekarar ’yan albashi ta 2015. Allah Ya sa mu ga karshenta lafiya.

Sai dai babban abin damuwa a wannan shekara shi ne yadda za a gudanar da zabubbuka a wannan shekara musamman a watan gobe watau na Fabrairu. Harkokin siyasa sun fara zafi, jam’iyyu sun fara yin kamfe. Allah Ya sa dai a yi zabe lafiya kuma a kafa gwamnati cikin nasara. Yana da kyau duk wadanda suka fadi a zabe su rungumi kaddara, don yin haka ne kadai zai samar da dauwamammen zaman lafiya ga kasar nan musamman a wannan lokaci da harkar tsaro ta tabarbare.
Ina kira ga Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta gudanar da sahihin zaben da kowa zai amince in kuwa ba haka ba, to akwai alamar za a iya samun matsala.
Talakan Najeriya da wanne zai ji? Da rashin kudi ko rashin tsaro ko kuma da matsalar tashe-tashen hankula?
Daga Muhammadu Sani Shokin
Sarkin Samarin Tudun Wada, Kaduna
08028797882

Sakonnin waya

Kira ga malaman Najeriya
Haba malaman Najeriya, ku ji tsoron Allah, ku bar zargin jumna, domin kun fake da wa’azin da kuke yi, kuna zagin juna. Abin takaici malaman darika na zagin Izala, malaman Izala na zagin darika. Mu lura mun rabu a masallaci, mun hadu a layin zaben siyasa. Mun rabu a makarantu, mun hadu a gidan gwamnati. Mun rabu a auratayya, mun hadu a kasuwa. Mun rabu a makabarta, mun hadu a Ka’aba. Mun rabu a kungiya, mun hadu a Kalmar “La Ilaha illalah.” Haba malaman Najeriya! Kar ku mayar da kanku jahilai mana! Ku Diana kafirta junanku. Ina yi wa al’umma Musulmi fatan alheri da fatan mun yi Mauludin Manzon Allah lafiya. Allah Ya ba mu zaman lafiya a kasar mu Najeriya. Daga Sayyada Fatima 08114300018.

Ga ’yan mata
Edita, ina kira ga ’yan uwana mata su daina yarda ana yaudararsu suna kai hare-haren kunar bakin wake, da ke salwantar da rayuka. Allah Ya kawo mana karshen wannan bala’i. Kuma wannan shekarar nasara ko ta Gregory da muka shiga, Allah ya ba mu albarkar da ke ciki, ya kuma tsare mu daga sharrin da ba mu sani ba. Rabbana takkabal minna. Amin. Daga Shamsiyya Kano 08139602473.

A kawo dauki Filato
Salamu alaikum. Editan Aminiya, don Allah ku tura wakilinku zuwa garin Aningo Pandam da Namu, a cikin Jihar Filato, domin ya ga abin tausayi, inda mata da kananan yara ke cikin tsaka mai wuya. Muna kira ga mawadata da su kawo musu dauki. Su tuna a duniya ake neman lahira. Duk inda ake tarzoma, su ciyar daga abin da Allah Ya wadata su da shi. Wallahi abin ya ba ni tausayi, Allah Ya ba da ikon taimakawa. Amin. Daga Sa’idu Ishak a dankanam, Gora, Jihar Nasarawa 08110995574.

Addu’a ga kasata
Assalamu alaikum. Ina addu’a Allah ya zaba mana shugaba nagari, mai tausayin, mai jin kai, wanda zai so Najeriya da al’ummarta, Musulmi da Kirista da marasa addini. Amin. Daga Usman Magaji, Kalgawai, karamar Hukumar Auyo, Jihar Jigawa 080663437074.

Ga PDP
Salam. Tsokaci za mu gani ko Jonathan zai je yankin Arewa, don gudanar da kamfe tunda bai je ya yi musu jaje ba. In kuma ya je za mu gani, wacce irin tarba za su yi masa, musamman ma ’yan Chibok. Daga Sa’adu Abdullahi Kaduna 08129296999.

Ta’aziyya ga rediyon Jigawa
Aminiya don Allah ku mika sakon ta’aziyya ga kungiyar zabi sonka ta Jihar Jigawa, da kuma hukumar gidan Rediyon Jigawa, bisa rasuwar Binta Yahaya Hassan. Allah Ya jikanta, Ya gafarta mata, kuma Ya bai wa ’yan uwnata hakurin jure rashinta. Daga Isa Sani Mai arsenal Garkon Alli, Jihar Jigawa 08062332784/08072556844.

Ina ake samun tallafin karatu?
Edita da kuma marubuta a wannan shafi. Sunanan Ibrahim Hussaini mazaunin Kaduna Sabon Gari, T/Wada. ’Yan uwa a nemo mana kungiyoyi da daidaikun mutane da ke bayar da tallafin karatu da biyan kudin makaranta ga ’ya’yan marasa galihu. Daga 080641292090.

A tanadi katin zabe
Ku tasbbatar kuna da rajista, don kare hakkinku, ba wai son Buhari ba, amma ba ka da rajista. Allah Ya sa Janar Buhari da jam’iyyarsa ta APC su kai ga gaci, su kuma fitar da ’yan Najeriya kunya. Amin. Daga Usman Gadodamasun Uke Jihar Nasarawa 09033322244.
Aminiya a Maradi
Salam Edita ka ba ni dama in yi murna kan nasarorin da Aminiya ke samu, domin ba a Najeriya ba, har ma a Jamhuriyar Nijar. A Maradi ba mu da abin da za mu ce, sai dai Allah Ya kara daukaka Aminiya. Daga Hon. Shamsu Muhammad Katsina 07039878892.

Ga Aminiya
Aminiya ina yi muku murnar sabuwar shekara 2015. Muna godiya a gareku. Daga Bello S.S. Matawalle 08106949703.

Ga Sanata Lado
Zuwa ga Sanatya Lado, mu al’ummar kaura Goje ba mu taba cin gajiyar aikinka ba. Saboda haka ya kamata a dube mu, tunda kai ne Sanatan Kano ta tsakiya, ta yadda mu ma za mu gnai, mu yaba maka. Daga Nazifi Musa Sale, Filin Alkama Gama (E). 08034285431.

Ga Janar Buhari
Edita a sanar da Janar Muhammadu Buhari, cewa, kowa nasa ne, amma dai akwai ’yan PDP da masu fakewa a bayansa. Mu dai fatan mu Allah Ya ba shi nasara don ya dawo da matabar talaka da mai kudi a kasar nan. Kowa naka ne. Allah Ya yi mana zabi mafi alkhairi. Amin. Daga Nasiru Bafulatani 08034836103.
Ga Shugabannin Arewa
Salam. Edita ka ba ni dama in yi kira ga tsofaffin shugabannin Arewa, su yi wa Allah su dubi halin da muke ciki. Don Allah su mara wa Buhari baya. Arewa muna cikin wahala. Daga Musbahu Yaro kokiya, karamar Hukumar Shanono, Jihar Kano. 07039042644.
Ga masu sayar da kuri’a
Edita, don Allah a ba ni dama inyi magana ga masu son kudi, musamman ma mata na ga da lokacin zabe ya zo sai ka ga abin ya koma kamar siyasar sayar da kuri’u. Wannan ai babban abin kunya ne. Wallahi in fada muku wani abu? To sayar da ra’ayinka da damarka saboda da kudi bai dace ba. Ku duba shekara hudu a Naira 100 tabdi jam! Kudi sun lalace. Gaskiya wnanan ma hauka ne. Allah ya zaba mana shugabanni nagari. Daga Isma’il Lawal Bakori 08032619334.
Mu canza gwamnati
Edita maganar gaskiya kowa yana son zaman lafiya, don haka ’yan Najeriya, maza da mata, kirista da Musulmi kada mu zabi PDP. Jam’iyyar PDP ba za ta iya kawo karshen matsalolin kasar nan ba. Jama’a mu hada kai, mu canza gwamnati. Daga Sa’adu dan Malam, mazaunin Kaduna 08129296999, 09030055445.