✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fatan alheri ga Falasdinawa

Yadda muka ji cewa bayin Allah Falasdinawa sun fara zama da abokiyar kai ruwa ranar su isra’ila, abinda matukar ban sha awa, domin duk da…

Yadda muka ji cewa bayin Allah Falasdinawa sun fara zama da abokiyar kai ruwa ranar su isra’ila, abin
da matukar ban sha awa, domin duk da cewa sun dade suna zaman doya damanja wanda sau da dama sukan kai farmaki wa juna inda ko wannebangare ke son samun galaba, a wannan karon muna yi masu fatan su cimma abin da zai ba da dama wato samun daidaito ? Na fadi hakan ne domin duk wanda zai yi adalci ga wannan batun zai ce Amurka ita ce mai ruwa da tsaki wurin dorewar hakan ko kuma akasin sa. Duka dai fatan mu Allah ya ba su ikon yin abin da zai zamo masu maslaha, amin.
Daga mukhtar ibtrahim saulawa katsina, 07066434519-08080140820

Sakonnin waya

Ga Gwamnan Neja

Zuwa ga Babangida Aliyu, Ma’aikatan Jihar Neja na shan ukuba a hannun gwamnatinka, saboda rashibn biyanmu kammalallen tsarin nan na albashin Naira dubu 18. Duk da alkawuran da ka sha dauka kana sabawa. Ka ji tsoron Allah ka biyamu. Ka kuma san akwai gobe. Daga Sani Tanko Unguwar Masallaci Suleja 08055164268.

Hattara matasa
Matasa wasu ’yan siyasa marasa kishin kasa, marasa kishinku na yin amfani da ku ta hanyar baku maye da shaye-shaye sannan su sanyaku badala da bangar siyasa don su ci zabe. Matasa ku tuna duk wanda zai sanyaku bangar siyasa da tada hankali ta hanyar baku kayan maye. In ya tura ku bangar siyasa, ku ce ya tura ’ya’yan da ya Haifa. Daga Amiru Isa Bakori 08075959086.

A yi sallah cikin natsuwa
Ko shakka babu akwai bukatar ‘yan uwa matasa mu gudanar da bukukuwan sallarmu, ta hanyar kauce wa duk wani abu da bai dace ba a lokacin gudanar da wannan buki. kama daga yin tukin ababen hawa cikin natsuwa banda yin gangancin dake iya jefa rayuwarmu cikin wani munmunan hali.inda a bangare daya akwai kyautatowar mu sanya sutturun da sunka dace da addininmu na islama  dama kyawawan al’adunmu,tare da kauce wa sanya ashararun tufafin da kwata-kwata sun yi hannun riga da koyarwa ta gari.daga karshe nake rokon Allah ya nuna muna zuwan wannan sallah lafiya tare da yin bukukuwan cikin kwanciyar hankali da Nishadi. Allahumma amen.
Daga Abdulmalik Saidu mai biredi tashar Bagu Gusau.

Ga Sanata Gamawa
Zuwa ga Sanatan Bauchi ta Arewa, Babayo Garba Gamawa ka san cewa talakawa suka zabeka, tun kafin lokacin lallaminmu ya zo. Domin ya kusa zuwa. Daga Danso Fatara Azare 08138746876.

Barka da sallah
Aminiya ’yar amana ku mika mana barka da salla ga ’yan uwa Musulmi da kuma ajgoran Jam’iyyar APC na kasa, kuma shugaban kasa a 2015 insha Allah. Janar Muhammad Buhari. Barka da Sallah. Da fatan za a yi bimkin sallah lafiya. Daga Musa Unguwar Maiyasin danja, Jihar  Katsina 08155648155.

Ga AbdusSamad Ishak Rabi’u da Barista Ibrahim Bello Rigachikum
Assalamu alaikum. Edita don Allah ka isar mani da sakon godiya ta musaman ga wadannan byin Allah masu jinkan bayin Allah, bisa tausaya wa  daurarru da suka yi na biya musu bashi da suka yi, wato Alhaji AbdusSamad Ishak Rabi’u da takwaransa , wato dan majalisar tarayya mai wakiltar da mazabar Igabi a majalisar wakilaio da ke Abuja, Barista Ibrahim Bello Rigachikum. Allah Ya saka da alheri, bisa wannan abin alheri da suka yi a gidajen yarin kasar nan. Dasga AbdurRashid Ahmad Mustapha Birnin-Gwari, Abuja 08093535622/08167671842.

Ta’aziyyar Sheikh Isa Waziri
Sakon ta’aziyya ga iyalan Wazirin Kano Malam Isa Waziri. Allah Ya kai rahama kabarinsa. Amin. Daga AbdulRazak danjuma T/Maliki Zoo Rd, Kano 08059211711.

Barka da sallah
Assalamu alaikum. Edita barka da warhaka ya aiki? Da fatan kai da iyali gami da abokan aiki duk kuna cikin koshin lafiya? Bayan wannan ina yi wa dukkan Musulmin duniya barka da kammala azumin watan Ramadan, tare da fatan Allah Madaukakin Sarki ya akrbi ibadunmu, Ya kuma sa muna da rabon ganin na badin badada da koshin lafiya, cikin imani. Amin. Daga Rabi’u Daudfa (KGY) Bindawa 08055552897.

Ga maza da mata
Gani gareku maza da mata. Me yasa Hausawa ke cewa idan saurayi da budurwa sun yi aure, sai a ce soyayya ta kare, sai dai zaman hakuri? Yanzu laifin mace ne ko na namiji? Daga Salihu Sama’ila Gitata, Jihar Nassarawa 08075356352.

Ga Buba Galadima
Aminiya don Allah ina son ku b ani dama in yi kira ga Buba Galadima bisa yabon kansa da najki ya yi. Buba ya kamata ka sani cewa yabon kai dai jahilci ne, ya kamata ka bari jama’ su yabeka a kan gaskiyarka. BNa kai ka yabi kanka ba. Daga Ibraheem Smart Yakasai Kano 08039700664.
Ta’aziyyar Wazirin Kano
Aminiya don Allah ku isar min da sakon ta’aziyyata ga iyalan Sheikh Malam Isah Waziri Kano, ga Maimartaba San Kano, Alhaji Dokta Ado Bayero da dukkan Mahammadawa, masoyan fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu Salallahu Alaihi Wassalam. Daga Mukhtar GZG 496 Pharmacy Makarfi, Jihar Kaduna. 07063321997.

Edita ka isar min da sakon ta’aziyyata ga Shugaban Majalisr Malamai da Maimartaba Sarkin Kano (Dokta) Ado Bayero da Gwamnan Kano bisa rasuwar Wazirin Kano Sheikh Isa Waziri haka kuma ian mika ta’aziyyata ga iyalan Sarkin Sharifan Kano, Sidi Fari. Allah Ya jikansu ya gafarta musu. Allah Ya bai wa iyualansu hakurin jure rashin. Daga alhaji Dubai G/Bajaj 07038605362.

Ayi salla lafiya
’Yan uwa da masoya da abokan arziki ina yi mana fatan mu yi sallah lafiya. Ramadan na yi mana bankwana. Allah Ya nuna mana wani ramada d aria da imani. Daga Nura Garba GGK Fatakwal 07039336645.