✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fasto ya bukaci ’yan kasuwa su rage farashin kaya don azumi

Shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen ECWA da ke Jihar Bauchi, Rabaran Muhammadu dan Amarya ya yi kira ga ’yan kasuwa da masu hannu…

Shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen ECWA da ke Jihar Bauchi, Rabaran Muhammadu dan Amarya ya yi kira ga ’yan kasuwa da masu hannu da shuni da su tallafa wa marasa karfi musamman a wannan lokaci na azumin Ramadan.

Faston ya kara da cewa, “azumi ibada ce da Allah madaukacin sarki Ya umarci dukkan Musulmi su yi don haka ya zamo wajibi a kan duk wani Musulmin kwarai da ya gyara halayensa tsakaninsa da al’umma. Da wannan nake fatan ‘yan kasuwa za su sassauta farashin kayayyan masarufi domin masu azumi su samu abin buda baki.
Tabbas malaman addinin musulunci sun fada cewa kyautata wa mai azumi yana da matukar mahimmanci a tsarin koyarwar addinin Musulunci, ”inji shi.
Ya yi fatan cewa Ubangiji nuna wa al’umma karshen watan lafiya kamar yadda ya nuna mana farkonsa. Har ila yau, ya yi kira ga Musulmi da su ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan. A wani labarin kuma, Shugaban kungiyar ’yan kasuwar Jihar Kebbi Alhaji dan Dare Mai Bulawus, ya ce watan Ramadan wata ne na afuwa da sauki wanda ya kamata ’yan kasuwa musamman Musulmi su yi rangwamen farashin kayayyakin masarufi albarkacin watan azumin Ramadan.
Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da makilinmu, ya ci gaba da cewa, manzon Allah (SAW) ya yi horo ga ’yan kasuwa da su tausaya cikin watan mai albarka domin al’ummar Musulmi su sami saukin saye da sayarwa.
Ya kara da cewa, “an sani cewa kayayyaki suna zuwa ne da tsada ko arha, amma babu dadi yadda wasu suke boye abubuwan da akafi bukata lokacin azumi domin su fito da su, su sayar domin cin kazamar riba, wadda yin haka halaka ce babba,” inji shi.
“Watan azumi, wata ne da ake son tausayawa da saukaka wa al’umma da taimako ta kowane fanni domin rabauta daga lada mai yawa a wurin Allah madaukakin sarki wanda azumi nasa ne.”
Daga nan ya yaba wa gwamnatin Jihar Kebbi akan aniyyarta ta taimakawa ’yan kasuwar jihar domin kasuwanci ya ci gaba da kuma niyyarta na kyautata wa rayuwar matasa. Ya ce: “Allah Ya ba ta ikon cika alkawurran da ta dauka, su kuma jama’a su taya ta da addu’a”.