✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fashewar wani abu ya jikkata Mutum 12 a Anaca

Akalla mutane 12 ne suka jikkata a tsohuwar kasuwar shanu da ke titin Akani, garin Anaca Jihar Anambara, sanadiyyar fashewar wani abu da ake kyautata…

Akalla mutane 12 ne suka jikkata a tsohuwar kasuwar shanu da ke titin Akani, garin Anaca Jihar Anambara, sanadiyyar fashewar wani abu da ake kyautata zato bam ne, a ranar Talatar da ta gabata.
Kasuwar mafiya yawancinta ’yan Arewa ne suke hada-hadar kasuwanci, inda suke sayar da shanu. Abin da ya fashe din, an ajiye shi ne cikin wata jarka da ake ajiye man fetur. Wani wanda ba a san ko waye ne ba ya ajiye ta, ya arce abinsa, kafin daga bisani ya fashe.
Wani mazaunin kasuwar da lamarin ya rutsa da shi kuma ya yi wa wannan jarida bayani, ya bukaci a sakaya sunansa ya ce: “Mu dai muna zaune yamma da masallaci sai muka ji fashewar wani abu daga bangaren gabas da inda muke zaune, da masallacin da abun ya tashi. Kowa sai ya yi ta kansa domin tsira da ransa, kowa sai ya ruga a guje, wasu a garin gudun ne suka samu raunuka da daman gaske. Babu wani wanda ya mutu amma bayan kura ta lafa an kwashi mutane, ni na gani an nufi asibiti da su.”
Ya ci gaba da yin karin bayani dangane da wadanda suka jikkatan: “Maza da mata ne cikin wadanda suka samu raunukan, akwai mata hudu daga ciki, sannan na ga maza guda takwas da wani yaro daya wadanda suka ji rauni.”
dan kasuwar ya ce tsammaninsu ko bam ne ya fashe, shi ya sanya ma kowa ya gigita, don gudun kada ya fada wa kaddara.
Sai dai ga dukkan alamu hakan na zuwa ne daidai da lokacin da kungiyar ’yan kabilar Ibo ta bai wa ilahirin al’ummar Fulani makiyaya wa’adin mako biyu da su tattara komatsansu, su fice masu daga yanki. Waje daya kuma wasu na hangen duk fa wannna lamari adawa ce ta siyasa da kuma nuna kabilanci ga Shugaban kasa, ganin cewa shi ya fito daga kabilar ta Fulani ce. Duk da cewa babu tartibin wani da ake zargi a halin da ake ciki, ya zuwa rubuta wannna labara, wasu daga cikin ’yan kasuwar ’yan Arewa sun yi gudun hijira zuwa garin Asaba, Jihar Delta. Amma kura dai ta lafa, babu wani rahoto ko bayani da ya nuna an bi su da bita-da-kulli.
Yanzu haka dai an baza jami’an tsaro a harabar wannan kasuwa, yayin da wasu kuma daga cikin ’yan kasuwar da ba su tsallaka Asaban ba suka ci gaba da gudanar da harkokinsu.
Aminiya ta tuntubi Kwamishinan ’yan sandan Jihar Anambara, Mista Hosea Kama game da afkuwar lamarin, bayan da ya ziyarci wurin da abin ya faru. Ya ce: “An sanya abun fashewar ne a cikin goran ruwa, sai aka sanya shi a cikin jarkar da ake zuba man fetur, aka zo aka ajiye. Sai kawai ya kama da wuta. Sai dai mutum goma ne suka samu raunin kuna, an kai su asibiti. Wannan shi ne abin da ya faru amma babu wani wanda ya rasa ransa.”