✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fargabar Hari: Sufeton ’Yan Sanda Ya Ba da Lambobin Kiran Gaggawa

A shirye 'yan sanda suke su dakile duk wata barazana da ka iya tasowa.

Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya fitar da wasu lambobin kira na gaggawa, da nufin dakile duk wani harin da ‘yan ta’addan za su iya kawo wa.

Baba ya ce rundunar na aiki tare da sauran jami’an tsaro, domin tabbatar da tsaron ’yan Najeriya.

Ya ja hankalin ’yan kasar cewa gargadin da Gwamnatin Amurka ta yi na cewa ’yan ta’adda za su kai hari a Abuja ba gaskiya ba ne.

Ya kuma bukaci daukacin ‘yan sanda da ke fadin kasar, da su karfafa tsaro a yankunansu, musamman a Abuja, babban birnin kasar.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, Sufeto Janar din ya kuma ba da umarnin kunna dukkan lambobin kiran gaggawa a fadin kasar, dommin amsa kira daga al’umma yayin da bukatar hakan ta taso.

“Ana kira ga mazauna Abuja da su bude idonsu sosai, tare da gaggawar kiran wadannan lambobi na layukan gaggawa: 08032003913, da 08061581938, da 07057337653, da kuma 0802894083.

Usman Baba ya kuma ce babu wani abin fargaba a Abujan, tare da umartarsu da su ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.

Kazalika, ya ce a shirye rundunar take ta dakile duk wata barazana da ka iya tasowa.