Farfesa Sagir Adamu Abbas ya samu nasara a kan abokan karawarsa guda uku a zaben share fagen zama Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano.
Farfesa Abbas wanda tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar ne ya samu kuri’u kimanin 1,026, inda ya doke abokin karawarsa na kurkusa, Farfesa Adamu Idris Tanko wanda ya samu kuri’u 416.
Zaben share fagen dai shi ne kusan mataki na kusa da na karshe, kuma galibi shi yake alamta wanda zai zama shugaban jami’ar a karshe.
Za a kammala matakan zaben ne ranar Asabar mai zuwa inda kwamitin zaben jami’ar zai tantance aya da tsakuwa tsakanin ‘yan takarar.
Sagir dai farfesa ne a bangaren Lissafi kuma ya fara aiki da jami’ar ne tun shekarar 1991 a matsayin mataimakin laccara har ya zuwa lokacin da ya zama farfesa
Ya taba rike mataimakin shugaban jami’ar har sau biyu, sai mukamin Darekta a Cibiyar Bincike da Kirkira ta Jami’ar (DRIP).
Kazalika, Farfesa Sagir ya taba zama babban mai taimaka wa tsohuwar ministar ilimin Najeriya, Farfesa Rukayya Rufa’i daga shekarar 2010 zuwa 2013.
Sauran ‘yan takarar da ya samu galaba a kansu sun hada da Farfesa Mohammed Dikko Aliyu da ya zo daga Jami’ar Sarki Fahad da ke kasar Saudiyya wanda ya samu kuri’u 10, sai Farfesa Dalhatu Balarabe Yahaya da ya samu kuri’u biyar.