Farashin waken suya ya fadi a wasu manyan kasuwannin hatsi na jihohin Filato, Kaduna da Kano da ke Arewacin Najeriya.
Wakilin Aminiya ya gudanar da bincike a babbar kasuwar hatsin garin Jingir da ke Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato, da babbar kasuwar hatsi ta garin Saminaka da ke Jihar Kaduna, da babbar kasuwar Hatsi ta garin Sabuwar Kaura da ke Karamar Hukumar Doguwa a Jihar Kano.
- Kwanan nan za a fara kashe kudaden Najeriya a China
- Yadda Liverpool ta yi wa Manchester United wankin babban bargo
Buhun sabon waken suya da aka sayar a makon da ya gabata kan N35,000 a wannan makon ya fadi zuwa N28,000.
Wakilinmu ya gano cewa kafin zuwa sabon waken suya na wannan kakar da aka shiga, sai da farashin buhun waken soyan ya kai N40,000.
Da yake zantawa da wakilinmu, wani dallali a kasuwar hatsi ta garin Jingir, Yakubu Yahaya Fedare, ya bayyana cewa a makon da ya gabata, an sayar da buhun waken suya a kan N35,000 amma a wannan makon ya fadi zuwa N28,000.
Ya ce shigowar sabon waken suyan ne, ya kawo faduwar farashinsa.
Sarkin Hatsin kasuwar Saminaka, Manu Isah Idris, ya bayyana cewa yawan da waken suya ya yi ne ya kawo faduwar farashinsa.
Har ila yau ya ce wasu kamfanonin da ke sayen waken sun rage farashin, wadannan su ne dalilan da suka kawo faduwar farashin waken suyar.