✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fararen hula 10 sun mutu bayan da motarsu ta taka bam a Burkina Faso

Mutum 10 sun mutu sakamakon taka bom da motarsu ta yi a gefen hanya.

Rahotanni daga kasar Burkina Faso sun ce fararen hula 10 sun mutu da dama sun jikkata bayan da motarsu ta taka bam.

An danganta aukuwar hakan da karuwar harkokin ‘yan tawayen da ke yaki da a kasar.

A cewar gwamnatin kasar, motar da lamarin ya shafa ta taso ne daga kasuwar garin Fada N’Gourma da nufin zuwa Kantchari da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar.

Gwamnan yankin, Kanal Hubert Yameogo, ya ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi da tsakar rana kusa da kauyen Bougui.

Bayanai sun nuna sama da shekara shida Burkina Faso na fama da rikice-rikicen da ake alakanta su da al-Qaeda da kuma ISIL, lamarin da ke ci gaba da yi wa zaman lafiyar kasar barazana.