Da sunan Allah, Mai tausayi, Mai jinkai.Dukkan yabo da godiya na Allah ne Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin bayinSa, Muhammadu danAbdullahi Balarabe, tare da alayensa da sahabbansa, masu daraja.
Bayan haka, yau tsokacinmu zai gudana ne kan falala da fa’idojin alwalla ga Musulmi. Kamar yadda kanun tsokacin ya nuna, alwalla ita ce daya daga cikin matakan shiga sallah. Amma kafin mu kawo fa’idojinta din, akwai bukatar mu gabatar da yadda ake yin ta, wanda shi ne kamar haka:
Farko dai bari mu dubi abin da Allah, Mai girma da daukakaYake cewa, a Alkur’ani Mai girma: “Ya ku wadanda suka yi imani! Idan kun yi nufin ku yi sallah, ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa gwiwoyi, ku shafa kawunanku da kuma (kuwanke) kafafuwanku zuwa idanun sawu….” Surah ta 5 aya ta 6.
Manzon Allah, sallallaahu alaihi wasallam, kuma ya ce, “Allah ba Zai karbi sallar kowane daya daga cikinku, wanda ya yi hadasi ba, har sai ya yi alwala.” Muslim ne ruwaitoshi.
Kafin ka fara alwala, za ka kudurta a ranka cewa za ka tsarkake kanka ta hanyar wanke gabban da ake wankewa, sannan ka ambaci sunan Allah, watau ka ce, ‘bismillaah’.
Sai ka wanke hannayenka zuwa wuyan hannu; ka kurkure baki; ka shaka ruwa a hancinka tare da fyacewa; dukan wadannan ayyuka sau uku-uku. Amma, a lura, abin da ya fi shi ne a hade kurkurar baki da shaka ruwa da fyacewar a wuri daya – watau idan an debi ruwan da hannu an kurba a baki, sai a rage dan wani a cikin hannun, sannan idan an kurkure bakin an zubar da ruwan, sai a shaki wanda aka rage din a cikin hannun daman, sai kuma a sa hannun hagu a fyace, kamar dai yadda ake fyace majina.
Sannan sai ka wanke fuskarka – sau uku (fadin fuska daga kunnen dama zuwa kunnen hagu; tsawon taku ma daga mafitar gashi ta al’ada zuwa karshen haba); daga nan sai hannayenka, na dama da na hagu, daga kan ’yan yatsu zuwa gwiwa – sau uku; sai ka shafa kanka da jikakkun hannayenka – gaba dayansa; sannan sai ka wanke kafafuwanka, na dama da na hagu – zuwa idanun sawu, sau uku-uku kowanensu (kana yi kan tsettsefe ’yan yatsun kafar da karamin dan yatsan hannu).
Shi ke nan ka gama alwala, sai ka daga kanka sama ka ce, ‘ashhadu an laa’ilaha illallaahu wahdahu laashareekalahu, wa ashhadu anna muhammadan ’abduhu warasuuluh’ wato Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Shi kadai Yake ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaida cewa Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa.Shi ke nan, sai a nufi wajen yin sallah.
To, kada mai karatu ya ce, “af, ai da ma ni haka nake yin alwalata, mene ne sabo a ciki?” In Allah Ya so nan gaba, muna fata bayanin da zai zo, zai kara wa mai karatu haske kan irin kura-kuran da ake aikatawa wajen rashin cika alwala – kamar yadda Manzon Allah, sallallaahu alaihi wasallam, ya bukaci a yi. Allah Ya ba mu dacewa!
Kafin mu kai ga hakan dai, akwai bukatar a karfafa kore batun wadanda ke cewa su Alkur’ani kawai suke bi wajen gudanar da sha’anoninsu na rayuwa da ibada. Muna cewa lallai masu irin wannan ikirari ba Alkur’anin suke bi ba, saboda idan mutum ya amince da wani sashe na shi (Alkur’anin), bai amince da wani ba, to bai amince da gaba dayansa ba. Allah Ya ce duk wanda ya bi Manzo, lallai ya bi Allah. Kuma duk abin da Manzo ya zo mana da shi, mu rike.Kuma lallai muna da abin koyi mai kyau a cikin al’amarin Manzon Allah… Kuma lallai ba za mu kasance masu imani ba, har sai mun alkalantar da Manzon Allah, sallallaahu alaihi wasallam, a cikin al’amurran da suke gudana a tsakaninmu, kuma mu bi, mu mika wuya mikawa a duk abin da ya yanke hukunci kansa, ba tare da nuna kyama ko ki ko wani kaikai game da abin a zukatanmu ba. A duba Alkur’anin a gani, za a gane wannan magana haka take!
A cikin ingantattun hadisai kuma ya yi nuni kan abin da ya zo da shi ba Alkur’anin ne kadai ba. Akwai wata hikimah (sunnah) tare da shi. Kuma duk abin da ya karantarko ya aiwatar ko ya gani ya kyale ko ya hana, an bukaci mu aiwatar da shi gwargwadon ikonmu. A duba hadisan a gani, za a gane, sai dai in mutum yana da gafalallar zuciya ne! Allah muke roko Ya kiyaye mu daga fadawa cikin sharrin shaidan.
Bari mu shiga alwalar, mu kara bibiyar ayyukanta: Farko dai za a yi nufin (niyyar) kawar da abin (hadasi) da ya hana a yi sallah, sannan a ce bismillaah! Ayyukan da suka ga ba ci wankin fuska, wadda Alkur’ani ya fara da ita, sun hada da wanke hannaye biyu zuwa wuyan hannu, wadanda ake yi wa wankin da ake kira “wankin hannun makitsiya” wato a rika gwama su ana cudawa gaba daya – ba daban-daban ba, sau uku, ba sau uku-uku ba; sai kurkure baki da shaka ruwa da fyacewa, a lokaci daya – sannan a maimaita sau uku. Wato idan an debo ruwan a cikin hannu, aka kurba a baki aka kurkura, wato aka motsa ruwan a cikin baki sosai, sai a zubar. Shi kuma ruwan da aka dan rage a cikin tafin hannu, sai a shaka shi a hanci, gwargwadon yadda ake iyawa, amma an fi son a shaka ya shiga hancin sosai, matukar dai ba azumi ake yi ba. Daga nan sai a sanya hanci a tsakanin yatsun dan-Ali (manuniya) da babban dan yatsa, kamar yadda ake fyace majina da hannun hagu, sai a fyace. Za a yi irin wannan tsarin aiki sau uku.
A nan akwai bukatar a lura, wannan tsari shi ne mafi ingancin tsarin da aka daga Manzon Allah, sallallaahu alaihi wa sallam. Kuma masu dora tafin hannu a kan hanci kawai ko shafa ’yan yatsu ko abin da ya yi kama da haka da sunan sun shaka ruwa, su sani cewa ba su bin tsarin da aka ajiye a shari’a – su ji tsoron Allah su koma kan abin da yake daidai.
Mu kwananan, sai mako na gaba, in Allah Ya kai mu!
Falala da fa’idojin alwalla ga musulmi
Da sunan Allah, Mai tausayi, Mai jinkai.Dukkan yabo da godiya na Allah ne Ubangijin halittu. Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin bayinSa, Muhammadu…