Ranar Juma’ar makon shekaranjiya, komai ya tsaya cak a Karamar Hukumar Hukumar Bici, da ma Jihar Kano baki daya, saboda yadda masu fada-a-ji a al’umma suka yi wa yankin tsinke don halartar daurin auren dan Shugaba Muhammadu Buhari, Yusuf, da Gimbiya Zahra Bayero, ’yar Sarkin Bici Nasiru Ado Bayero.
Shugaba Buhari ne ya jagoranci bakin nasa, wadanda wane-da-wane ne a fagen siyasar Najeriya.
Wadannan baki sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, da Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, da babban abokin hamayyar Shugaba Buhari a zaben 2019, Atiku Abubakar.
Sauran sun hada da gwamnoni, da shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa da sauran ’yan majalisar, da ministoci da sauran masu rike da mukaman siyasa.
Sannan akwai sarakunan gargajiya da manyan ’yan kasuwa.
Ayarin jiragen sama na kashin-kai da dama ne suka sauka aka kuma jere su a Babban Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, yayin da aka tuka wadannan baki a motocin zamani na-gani-na-fada zuwa wurin daurin auren, wato Babban Masallacin Juma’a na garin Bici.
Kyaututtukan da aka raba a wurin sun hada da waya kirar iPhone 12 Pro Max, wadda ta fito kwanan nan, kuma ake sayar da ita a kasuwa a kan kudi N589,000, da Apple iPad, wanda ake sayarwa a kan kudi N645,000 da sauransu.
Hakazalika ga abinci nan iri-iri sai wanda mutum ya gani.
Bukukuwan da suka gabaci daurin auren sun hada da wasan kwallon polo na musamman da wankan amarya, inda adon gwalagwalan da aka yi wa rigar amarya ya sa mahalarta sake baki.
Ko da yake mun gamsu cewa iyaye suna da hurumin da za su shirya wa ’ya’yansu irin bikin da ya yi wa zuciyarsu dadi, amma hakan bai kamaci shugaban kasa ba, musamman ma shugaban kasa mai ci, wanda ake ganin mutum ne mai zuhudu.
Daya daga cikin halayen Shugaba Buhari da suka cusa wa ’yan Najeriya kaunar sa gabanin zaben 2015 shi ne saukin kai; ga shi kuma ba ya son almubazzaranci.
Shi ya sa hotunan abubuwan da suka faru a Bici suka sa mutane kaduwa da takaici.
Babu shakka abin da ya faru facaka ne, kama daga yadda baki suka halarci wurin zuwa ga irin abincin da aka baje da ma kyaututtukan da aka raba, sai dai idan hotunan da aka wallafa a kafofin sada zumunta ba na gaske ba ne.
Gaba daya bikin na nuni da dagawa. Kuma ko a nan aka tsaya, ba abu ba ne da ya dace a kasar da ake yi wa kirari da hedikwar talauci ta duniya.
Kai, wannan lamari ya yi muni, musamman ma a wannan lokaci da har yanzu wasu mutane ke fama da karayar arziki sakamakon annobar coronavirus.
Da kyar da jibin goshi ’yan Najeriya da dama suke samu su ci abinci sau uku a yini; wadanda suke samu din ma – a dai yi sha’ani kawai.
Bugu da kari, miliyoyin iyalai na gwagwagwa da biyan kudin asibiti ko na makarantar yara.
Wani abin dubawa kuma shi ne wannan lamari ya faru ne a karkarar Jihar Kano ta Arewacin Najeriya, yankin da ya fi ko’ina talauci a kasar nan.
Sannan baya ga fama da talauci, mutane na dandana kudarsu saboda rashin tsaro.
Alal hakika, a daidai lokacin da ake daurin auren, yaran da aka sace daga wata makaranta a Tegina, Jihar Neja, na hannun masu garkuwa da mutane, haka ma daliban makarantar Bethel da aka sace a Kaduna.
Don haka, akwai alamun nuna rashin damuwa da halin ni-’ya-sun da ake ciki a shirya irin wannan biki a daidai lokacin da kasar ke cikin yanayin alhini.
Kamata ya yi a ce shugaban kasa ya shirya bikin da bai kai wannan kasaita ba, kamar wanda ya shirya bara, lokacin da ya aurar da ’yarsa.
Hujjar cewa wasu abokan arziki ne suka dauki nauyin kyaututtukan da aka raba da bukukuwan da aka yi ba ta ma taso ba sam, don kuwa bai ma kamata ba a ce shugaban kasa yana amincewa da haka, duba da akidarsa.
Ba za mu wuce ba sai mun ambaci gwamnoni, wadanda galibinsu suka je daurin auren a jiragen saman a kashin-kai, duk da cewa ma’aikatan jihohinsu na bin su bashin albashi.
Bai kamata ba a rika daukar daurin auren wani shugaba na siyasa a matsayin aikin gwamnati wanda za a yi amfani da kayan hukuma don aiwatar da shi.
Wajibi ne a daina wannan daga yanzu.
Mai yiwuwa mu yi tunanin ai an yi auren komai ya wuce, amma a zukatan mutane da dama lamarin ya kara fadada bambancin da ke tsakanin masu shi da marasa shi.
Gaskiya ne cewa ko ’yan yatsunmu ba tsayinsu daya ba, kuma galibin mutane talakwa ne, amma bai kamata a rika nuna musu dagawa ba.
Wani karin hadari da wannan lamari ka iya haifarwa shi ne zai sa wasu su kuduri aniyar tara dukiya ta ko wacce hanya, ciki har da halal ya ki, haram ya ki.
Wajibi ne shugabanninmu su rika nuna damuwa da halin da mutane ke ciki, su kuma rika taka-tsantsan yayin irin wadannan bukukuwa don kauce wa mummunar fahimta da tunzura jama’a.