✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ezekwesili zata yi takarar shugabar Najeriya

Bayan zaben fidda gwani da aka yi na nemar tikitin takarar zaben shugaban kasar Najeriyar a 2019 an tsaida tsohuwar Ministar Ilimi kuma shugabar ayarin…

Bayan zaben fidda gwani da aka yi na nemar tikitin takarar zaben shugaban kasar Najeriyar a 2019 an tsaida tsohuwar Ministar Ilimi kuma shugabar ayarin gidauniya ‘Bring Back Our Girls’ Oby Ezekwesili a jam’iyyar ACPN.

Jam’iyyun  ‘New Nigeria Peoples Party (NNPP), Accord (A), Allied Congress Party of Nigeria (ACPN), Zenith Labour Party (ZLP), Peoples Coalition Party (PCP) da Advanced Nigeria Democratic Party (ANDP)’ sun hada kai wajen fitar da ‘yar takarar da zata wakilce su a zaben shugabar Najeriya.

Jam’iyyun sun yanke shawarar ne jiya a Abuja don cika wa’adin hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta bayar.