Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta bi sauran takwarorinta wajen yin Allah wadai da matakin da Koriya ta Arewa ta dauka na harba makami mai linzami a sararin samaniyar Japan a ranar Talata.
A cewar kakakin kungiyar wannan ba komai bane face takalar fada, wanda ya yi hannun riga da ka’idojin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.
- Rayuwar Dabbobi: Tattabara uwar alkawari
- DAGA LARABA: Yadda Yawan Harsuna Da Kabilun Najeriya Zai Amfane Ta
EU ta ce dole ne Koriya ta Arewa ta guji harba makamai a sararin samaniyar wasu kasashe, bugu da kari ta kuma ba da damar hawa teburin sulhu domin tattauna duk wasu matsaloli da take da su a game da kasar ta Japan.
Kazalika EU ta kuma bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya duba da ma daukar mataki a kan irin barazanar da wannan harba makamai ke daga kasashe makwabta da ma batun tsaron yankin baki daya.
Wannan shi ne karon farko a cikin shekaru biyar da Koriyar ke harba wa Japan makami mai linzami, lamarin da ya sa ake tunanin akwai wata jikakiya a kasa.
Makamin mai linzamin wanda ya ci tafiya mai tazarar kilomita 4,500 zuwa 4,600 ya fada a Tekun Pacific.