✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Eritiriya ta koma cikin Kungiyar IGAD

Ta shafe kusan shekara 16 a matsayin saniyar ware a tsakanin kasashen yankin.

Kasar Eritiriya ta koma cikin Kungiyar Hadin-kan Kasashen Gabashin Afirka (IGAD), bayan shafe kusan shekara 16 a matsayin saniyar ware a tsakanin kasashen yankin.

A shekarar 2007 Gwamnatin Eritiriya ta dakatar da kasancewarta mamba a Kungiyar IGAD, bayan ta samu sabani da sauran mambobin kungiyar a kan al’amura da dama, ciki har da kokarin warware rikicin kan iyaka a tsakaninta da Habasha, kasar da ta balle daga cikinta a 1993.

A 2021 Amurka ta kakaba wa Eritiriya takunkumi bayan ta tura dakaru zuwa yankin Tigray da ke Arewacin Habasha, domin mara wa sojojin Habasha baya, sai kuma zargin da ake yi wa dakarunta na kashe daruruwan fararen hula a yakin Tigray.

Eritiriya ta kasance karkashin jagorancin Mista Isias Afwerki tun bayan samun ’yancin-kai daga Habasha a 1993, inda ta shafe tsawon shekara 2 tana yakin kan iyaka da tsohuwar uwargijiyarta daga 1998 zuwa 2000, kafin a yi sulhu.

A 2018 Eritiriya ta kawo karshen rikicin da ke tsakaninta da Habasha, ta kuma gyara alakarta da kasashen Somaliya da Djibouti.