Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai ziyara Jihar Legas domin jajantawa bisa asarar da aka yi a jihar a lokacin tarzomar zanga-zangar EndSARS.
Sarki Aminu Ado Bayero, yayin ziyararsa ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce, duk abin da shafi Legas, to ya shafi Kano.
- Arewa ta kira taron tsaro bayan ‘katobarar gwamnati’ kan kisan Zabarmari
- Wani mutum ya mutu bayan ya kashe makwabcinsa
“Na zo ne don yin jaje da kuma da fatan alheri a madadin Gwamnati da al’ummar Kano ga Gwamna da kuma Oba na Legas wanda uba yake a gare ni; yana da muhimmanci mu jajanta wa duk wanda abin da ya faru a makonnin baya ya shafa.
“Dadaddiyar dangantakar da ke tsakanin Legas da Kano ta sa duk abin da ya samu Legas to ya shafi Kano”, inji Sarkin Kano.
Ziyarar ita ce ta farko da Sarki Aminu Ado Bayero ya kai zuwa Jihar Legas tun bayan zamansa Sarkin Kano a watan Maris, 2020.
Ya ce ya kai ziyarar da kansa ne domin janjanta wa gwamnan kasancewar jihohin biyu sun yi tarayya ta fuskar kasuwanci da kuma sarauta.
“Na gana da Oba da kuma Gwamna kuma mun fahimci juna ta yadda hakan zai kyautata dangantakar da ke tsakanin Kano da Legas na daruruwan shekaru”, inji Sarkin Kano Aminu.
Yayin ganawarsa da Gwamna Sanwo-Olu a gidan Gwamantin Jihar Legas da ke Marina, basaraken ya ce Kano ta shiga cikin damuwa a lokacin da ta samu labarin irin tashin hankalin da asarar da tarzomar ta haifar a Legas.
Ya kara da cewa makasudin ziyarar shi ne karfafa dangantaka tsakanin Masarautar Kano da masarautun Kudu maso Yammaci, inda ya ce ya samu ganawa da sarakunan a Abeokuta, Ibadan, Oyo da Ile Ife a lokacin ziyarar.
Sarkin ya bayar da tabbacin cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da karfafa dangantakar da ke tsakaninta da jihar Legas; inda ya jaddada muhimmancin hadin kan Najeriya.
Ya kuma yi kira ga matasa da su nisanci tashin hankali su rungumi zaman lafiya domin amfanin daukacin al’umma.
Sarkin Kano ya kuma bukaci ’yan siyasa da su gaggauta daukar matakan magance matsalolin da suka haifar da zanga-zangar ta EndSARS.
Da yake mayar da jawabi, Sanwo-Olu ya yi godiya ga sarkin game da ziyarar da kuma dangantakar mai ‘tarihi’ tsakanin Legas da Kano.
Gwamnan ya ce ziyarar za ta taka muhimmiyar rawa wajen kyautata dangantaka tsakanin jihohin biyu sannan ya yi alkawarin Gwamnatin Jihar Legas za ta ci gaba da kare muradun bangarorin biyu.
Ziyarar jajen da Sarkin ya kai ta biyo bayan kashe-kashe, kone-kone da barnata kadarorin al’umma da gwamnati da aka yi a Jihar Legas, lokacin zarga-zangar da bata-gari suka mamaye ta koma tashin hankali.
Sarkin ya bayar da tabbacin cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da karfafa dangantakar da ke tsakaninta da jihar Legas; inda ya jaddada muhimmancin hadin kan Najeriya.