Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong, ya ce gwamnatin jihar ta yi asarar dukiyar kimanin biliyan N75, a tsakanin ranakun Asabar da Lahadin da masu zanga-zangar #EndSARS suka yi sace-sace a fadin jihar.
Wakilin Aminiya da ke jihar, ya bayyana cewa masu satar kayayykin ba su tsaya ga iya kayan gwamnati ba, sun hada da wuraren ajiyar kamfanoni masu zaman kansu.
- Ganduje ne jagoran yaki da cin hanci a Najeriya —Salihu Tanko Yakasai
- Satar kayan tallafi: An samu gawar hudu a cikin dam
- Ana tsine min a masallatai saboda #EndSARS —Aisha Yesufu
“Sama da mutum 100 muka samu rahoton dakarun rundunar OPSH sun kai musu hari yayin da suke sace muhimman kayayyaki a jihar”, inji shi.
Da yake ganawa da wasu matasan da lamarin ya ritsa da su a jihar, Lalong, ya ce, “Rahoton da muka samu a baya-baya nan daga wani kwamatin kwararru da na kafa, shi ne an tabka asarar dukiyar da ta kai naira biliyan 75 kawo yanzu.
“Faruwar wannan al’amari ka iya mayar da jihar baya, za mu shafe yi shekaru ba mu iya mayar da abun da muka rasa ba, saboda bamu da halin mayar da abun da muka rasa a yanzu na gine-ginen da aka lalata da wanda aka barnatar ko aka sace.
“Har yanzu ba mu gama wartsakewa daga tabarbarewar tattalin arziki da muka samu ba sakamakon annobar COVID-19 wanda ya taba mu sosai.
“Muna da akalla hukumomi da ma’akatun gwamnati da masu zaman kansu da abun ya shafa kimanin 32 da aka barnatar da lalatawa da sace kayayyinsu a zanga-zangar #EndSARS”, kamar yadda gwamnan ya yi karin haske.