Kafafen yada labaran duniya sun bayyana rasuwar sarauniyar Ingila, Elizabeth a ranar Alhamis, tana da shekaru 96 a duniya.
Rahotanni na cewa danta da ya gaje ta, Yarima Charles, da ‘yan uwansa da sauran manyan masu fada a ji, sun kasance a kusa da mahaifiyarsu har zuwa lokacin da ta rasu.
- Yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya yanzu ya kai miliyan 18 – UNICEF
- Mun gano kayan sojoji da tarin kudade a gidan Tukur Mamu – DSS
Ga wasu muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da marigayiyar:
- An haife ta a ranar 21 ga watan Afrilun 1926
- An haife ta a yankin Mayfair da ke birnin London, a matsayin ‘yar fari ga Sarki George na shida, da mai dakinsa, Sarauniya Elizabeth ta farko. Mahaifinta ya hau kan karagar mulki a shekara ta 1936 bayan murabus din dan uwansa, Sarki Edward na takwas.
- Lokacin da mahaifinta ya mutu a watan Fabrairun 1952, Elizabeth na da shekara 25, ta zamo sarauniyar da kasashe bakwai da suka hada da Burtaniya da Kanada da Australia da New Zealand da Afirka ta Kudu da Pakistan da Ceylon (Sri Lanka a yanzu0 ke karkashin mulkinta.
- A watan Nuwambar 1947 ne ta auri Philip Mountbatten, basarake daga kasar Girka da Denmark, kuma sun shafe shekaru 73 tare, har mutuwarsa a watan Afrilun 2021.
- Sun haifi ‘ya’ya hudu tare; Yarima Charles da Gimbiya Anne da yarima Andrew da Yarima Edward.
- Ta dare karagar mulkin kasar a shekarar 1953, sannan an gudanar da bukukuwan bikin cikarta shekaru 20 da 50 da 60 da 70 bi-da-bi a shekarun 1977 da 2002 da 2012 da 2022.
- Elizabeth ita ce sarauniya mafi dadewa a raye, da kuma kan karagar mulkin Birtaniya, sannan ita ce ta biyu a mafi dadewa a kan karagar mulki a tarihin duniya.
- Elizabeth ta yi sarauta bisa turbar tsarin mulki, da samar da manyan sauye-sauyen siyasa, da suka hada da magance matsalolin Arewacin Ireland, da kawo karshen mulkin mallaka a yankin Afirka, da ficewar Ingila daga kungiyar Tarayyar Turai.
- Ta sha fama da sukar kafofin watsa labaran duniyai game da danginta, musamman bayan mutuwar auren ‘ya’yanta, da bala`o`i daban-daban da suka faru da ita a shekarar 1992, musamman mutuwar surukarta Diana, wato Gimbiyar Wales, a 1997.