Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta yi gwanjon gidan tsohuwar Ministar Fetur, Diezanni Alison Madueke, da wasu katafarun gidaje da filaye 160.
Hukumar ta kada kararrawa ga kadarorin na biliyoyin Naira da ke unguwannin masu kumbar susa da ta kwato ne a jihohi 16, ciki har da Legas da Abuja.
- Majalisa ta bukaci CBN ya tsawaita wa’adin daina karbar tsohon kudi
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Tabbatar Da Zaman Lafiya A Harkokin Zabe
EFCC, wadda tun da farko ta yi gwanjon wasu motoci 649 da ta kwato a Abuja da Fatakwal da Ilorin da sauran wurare, ta ce kofa a bude take ga masu sha’awar sayen gidajen alfarmar har zuwa ranar 9 ga Janairu, 2023.
Ta ce, hatta mazauna gidajen da aka yi gwanjon nasu za su iya shigowa su saya, muddin ba su da wata matsala da hukumar.
Aminiya ta tattaro cewa, galibin kadarorin da hukumar ta kada wa kararrawa, ta kwato su ne daga jami’an gwamnatin da suka yi amfani da matsayinsu wajen karkatar da dukiyar al’umma.
Kadarorin sun hada da wadanda tsohon Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Kasa (NIA), Ayodele Oke, ya mallaka.
A ranar 15 ga Disamba, 2022, aka jiyo Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa na cewa, hukumar ta yi gwanjon motoci sama da 649 kuma ta shirya kada wa wasu tarin gidaje da filaye na biliyoyin Naira kararrawa don amfanin masu bukata.
Daga Bashir Isah, Simon E. Sunday, Philip S. Clement, Idowu Isamotu & Abbas Jimoh