Hukumar Hana yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa ta EFCC ta kulle wani gida mallakin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da ke titin Miller Road a Kano.
Sanata Kwankwaso dai ya taba zama Gwamnan Jihar Kano har sau biyu, kuma ya wakilci mazabar Kano ta tsakiya a Majilisar Dattijan Najeriya tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.
- Buhari ya sake sabunta wa’adin shugabannin JAMB da NUC da UBEC
- Ba mu amince da dakatar da Abba Kyari ba —Sheikh Jingir
Lokacin da Aminiya ta ziyarci wajen, wani wanda yake wurin lokacin da abin ya faru ya ce lamarin ya biyo bayan wata kara da iyalan tsohon Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkar Tsaro, Ismaila Gwarzo suka kai.
Ya ce iyalan sun yi zargin cewa wani mai suna Abdullahi Muazu Gwarzo da aka fi sani da Baba Gandu, wanda tsohon shugaban rusasshiyar Hukumar Kwashe Sharar ta Jihar Kano (REMASAB) ne ya sayar da gidan wanda mallakinsu ne ga Kwankwaso, sannan ya ki ya basu kudin.
“Lamarin rufe gidan wata matsala ce aka samu tsakanin iyalan marigayi Ismaila Gwarzo, Kwankwaso ya shigo ciki ne kawai saboda shi ne ya sayi gidan,” inji shi.
Sai dai har yanzu EFCC ba ta magantu a kan batun ba, amma Aminiya ta gano cewa hukumar na binciken tsohon Gwamnan kan zargin karkatar da kudaden Kananan Hukumomin Jihar da yawansu ya haura Naira biliyan uku lokacin yana Gwamna.
Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwajaren ya tabbatar wa Aminiya cewa hukumar na binciken zarge-zargen da ke cikin kunshin tuhumar.