Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta aika da wata wasika ta musamman ga kasar Guinea inda ta nuna kasar za ta iya cigaba da gudanar da wasannin kwallon kafa a kasar ba tare da matsala ba ganin yadda aka aka samu nasarar kawar da cutar ebola daga kasar.
Cutar Ebola dai ta addabi kasar ce a ’yan shekarun baya al’amarin da ya sa aka dsakatar da yin wasannin kwallo a kasar.
A wasikar da Sakatare-Janar na Hukumar CAF Hicham El Amrani ya rubuta wa Shugaban hukumar kwallon kafa ta Guinea Salifou Camara ya nuna yadda Hukumar ta amincewa kasar ta ci gaba da gudanar da wasannin kwallo a cikin kasar.
Hukumar kula da kiwon lafiya ta Majalisar dinkin Duniya (WHO) ce ta wanke kasar Guinea daga kamuwa da cutar Ebola a ranar 31 ga watan Disamban 2015, al’amarin da ya sa ita ma Hukumar CAF ta dage takunkumin da ta kakaba mata.
Idan za a tuna Hukumar CAF ta umarci Guinea ne ta koma wadansu kasashe da take makwabtaka da su wadanda ba a samu bullar cutar ebola ba wajen gudanar da wasanninta na gida a can. Kuma tun daga wancan lokaci ne kasar take yin haka sai a yanzu da aka dage mata tankunkumin.
Ebola: CAF ta dage takunkumin da ta kakaba wa Guinea
Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta aika da wata wasika ta musamman ga kasar Guinea inda ta nuna kasar za ta iya cigaba da…