✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dukan matar maƙwabci ya kai magidanci gidan yari a Kano

Ya ji wa matar maƙwabcinsa rauni a fuska da wasu sassan jikinta

An gurfanar da wani mutum a gaban kotun Musulunci kan zargin yi wa matar maƙwabcinsa dukan kawo wuƙa a Jihar Kano.

Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun da ke zama a unguwar Kurna Asabe cewa wanda ake zargin ya kuma ji wa matar auren munanan raunuka.

Ya yi wa matar wannan aika-aika ne bayan wata taƙaddama, inda ya ji mata munanan raunuka a fuska da wasu sassan jikinta.

Alƙalin kotun, Khadi Alhaji Jibrin Ɗanzaki, ya ba da umarnin tsare mutumin a gidan yari sannan ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga watan nan na Mayu.