✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk tsokar da ta ginu da haram wuta ce makomarta! (1)

Babban Masallacin Tabuka, Saudiyya Fassarar Salihu Makera Huduba ta Farko Godiya ta tabbata ga Allah, Ma’abucin girma da mulki, ina gode maSa Mai cikakken tsarki,…

Babban Masallacin Tabuka, Saudiyya

Fassarar Salihu Makera

Huduba ta Farko

Godiya ta tabbata ga Allah, Ma’abucin girma da mulki, ina gode maSa Mai cikakken tsarki, Shi ne Rayayye Wanda ba Ya mutuwa. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin kasa da sammai. Na shaida lallai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, Mai rayawa Mai kashewa kuma Shi Mai iko ne a kan dukan  komai. Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa, Ubangijinsa Ya zabe shi domin ya isar da sakonSa kuma ya shiryar da mutane baki daya. Mafificiyar tsira da mafi girman taslimi daga Ubangijinsa su tabbata a gare shi da alayensa da matansa iyayen muminai da sahabbansa masu daraja na hannun damansa da tabi’ai da wadanda suka biyo bayansu har zuwa Ranar kiyama.

Bayan haka ya zo a cikin Hadisin Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ya ku mutane! Lallai Allah Mai tsarki ne kuma ba Ya karbar aiki sai mai tsarki. Kuma Lallai Allah Ya umarci muminai da abin da Ya umarci Manzanni da shi, inda Ya ce: “Ya ku Manzanni! Ku ci daga tsarkakan abubuwa kuma ku yi aiki nagari. Lallai ne Ni game da abin da kuke aikatawa Masani ne.” Kuma  Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku ci daga tsarkakan abubuwan da Muka azurta ku.” Sannan ya ambaci wani mutum wanda ya fito daga doguwar tafiya, mai gizo (yawan gashin kai) mai kura, yana daga hannunwansa zuwa sama (yana cewa): “Ya Ubangiji! Ya Ubangiji! Alhali abincinsa haramun ne, abin shansa haramun ne tufafinsa na haram ne, an raine shi da haram. Ta yaya za a amsa masa?” Muslim ya ruwaito a cikin Sahihinsa.

A nan Manzon Allah (SAW) yana nuni ne kan hadarin cin dukiyar haram ta kowace irin hanya, kuma ko ta yaya aka same ta. Dukiyar haram tana hana karbar addu’a ta sa Allah Ya rufe wa mutum kofofin sama. Dukiyar haram hanya ce abar kyama mai cike da hadari da ke jefa ma’abucinta a cikin wuta! An karbo daga Jabir bin Abdullahi (RA) cewa “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk tsokar da ta ginu da haram ba za ta shiga Aljanna ba.” Tirmizi da wadansu suka ruwaito. Kuma Buhari da Ahmad sun  ruwaito daga Hadisin Haulatu Al-Ansariyya (RA) ta ce: “Na ji Annabi (SAW) yana cewa: “Lallai mutanen da suke kutsawa (suke aukawa) a cikin dukiyar Allah ba tare da hakki ba, suna da wuta a Ranar Alkiyama.”    

Don haka ya ku mutane! Ku guji cin dukiyar haram, domin ita mummunar kazanta ce kuma muguwar cuta ce, sannan hanya ce ta zuwa ga halaka da ingiza ma’abucinta zuwa ga wuta. Ku guji dukiyar haram ta kowace hanya ko siffa ta zo muku, ita kazanta ce. Kuma Allah Madaukaki ba Ya son kazanta. Allah Madaukaki Ya ce: “Ka ce: “Mummuna da mai kyau ba su daidaita, kuma koda yawan mummunan ya ba ka sha’awa. Saboda haka ku bi Allah da takawa ya ma’abuta hankula la’alla za ku ci nasara.” (Ma’ida:100).  Dukiyar haram da yawa Shaidan ke kawata ta ga mutane yana jan ra’ayin zukatan masu rauni daga cikin mutane zuwa gare ta.

Daga cikin dukiyoyin haram wadda ta fi girman hadari ga daidaiku da kuma al’umma da dauloli da kasashe, akwai mu’amala da dukiyar riba. Riba tana yanke albarkar dukiya ta cire alherin da ke cikinta. Allah Madaukaki Ya ce: “Allah Yana shafe albarkar riba, kuma Yana kara sadakoki. Kuma Allah ba Ya son dukan mai yawan kafirci, mai zunubi.” (Bakara:276). 

Riba tana daga cikin mafiya munin cututtukan da suke illa ga jama’a. Kuma ya alla ribar a tsakanin daidaikun mutane ne ko a tsakanin bankuna da kamfanoni. Riba, riba ce koda sunayenta sun saba ko fasalinta ya saba ko hanyar mu’amala da ita ta saba. Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa, kuma ku bar abin da ya rage daga riba, idan kun kasance masu imani. To idan ba ku aikata ba, (kuka hanu ba), to ku sani fa da akwai yaki daga Allah da ManzonSa. Kuma idan kun tuba to kuna da asalin dukiyarku, ba ku zalunta, kuma ba a zaluntarku.” (Bakara: 278-279). Don haka riba haramun ce ta duk yadda aka juya, kuma dukan tu’ammali da ita mai yawa ko kadan haram ne. Allah (SWT) Ya ce: “Kuma Allah Ya halatta kasuwanci kuma Ya haramta riba.” (Bakara: 275). 

Kuma tsoratarwa a kan hadarin riba ta zo a cikin Sunnar Almustapha (SAW) daga Jabir (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya la’anci maciyin riba da wanda aka wakilta a kai da mai rubutawa da mai bayar da shaida. Ya ce: “Su dukkansu daidai suke (cikin zunubi).” (Muslim ya ruwaito.)

Sannan ku sani -Ya ku mutane!- Riba ba ta taba halatta a karkashin shari’a, kuma babu wanda ya bayar da fatawa kan halaccinta, sai dai wanda ya daura yaki da Allah da ManzonSa (SAW), mai kuncin ilimi, mai wahalar gane gaskiya, mai bin son zuciyarsa, mai bata imaninsa, wanda ya yarda da fushin Allah. Mai tsira da amincin Allah ya ce: “dayanku ba ya yin imani har sai ya kasance zuciyarsa tana bin abin da na zo da shi.”

Riba haramun ce kuma daya ce daga cikin kaba’irai (manyan zunubai), kuma daya ce daga cikin manyan laifuffuka, tana halakar da dukiya ta kashe rayuka ta bata shuka da tsiro. Manzon Allah (SAW) ya ce: “A daren Isra’i na iske wadansu mutane da cikkunansu kamar gidaje, a cikinsu akwai majizai da ake iya gani daga wajen cikkunansu. Sai na ce: “Su wane ne wadannan ya Jibrilu? Sai ya ce: “Wadannan su ne maciya riba.” Ibn Maja ya ruwaito.

Kuma Mai tsira da amincin Allah ya ce: “Riba tana da kofofi saba’in, mafi saukinta, mutum ya yi zina da mahaifiyarsa.” Ibn Majah ya ruwaito. Don haka ya ku Musulmi ku guji riba a cikin mu’amalolinku da ayyukanku domin yaki da Allah Madaukaki ne, shin wane bawa ne zai iya yaki da Mahaliccinsa, Mai azurta shi, kuma Wanda Ya samar da shi?

Sannan daga cikin misalan dukiyoyin haram akwai dukiyar da ake yin rantsuwa da Allah bisa karya a kanta domin a tauye hakkoki ko a tara dukiya. An karbo daga Abu Umamah (RA) cewa: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda duk ya ci dukiyar wani Musulmi da rantsuwarsa, hakika Allah Ya wajabta masa wuta, kuma Ya haramta masa Aljanna.” Sai wani mutum ya ce masa: “Ko da dan kadan ne ya Manzon Allah!” Sai ya ce “Koda itacen goge baki ne.” Muslim da Nisa’i suka ruwaito, kuma lafazin na Nisa’i ne. 

Ku duba -ya ku mutane! – Yadda karbewa ko danne wa wani itacen aswaki bisa zalunci da haramci yake zama sababi daga cikin sabuban shiga wuta. Allah Ya tsare mu. To yaya lamarin zai kasance ga wanda yake kwacewa ko sacewa ko yake danne wa wani ko wadansu abin da ya fi aswaki? Hakika mujirimancinsa ya fi girma, kuma ukubarsa ce mafi girma!

Daga cikin mutanen yanzu, akwai wanda ba ya tsoron Allah Madaukaki, ba ya yi maSa takawa ba ya tsoron haduwa da Shi, inda za ka gan shi yana rantsuwa da Shi bisa karya da zalunci da gangan domin ya ci wani abu daga dukiyar haram, kuma ta yiwu rantsuwar da ya yi, ta zama dalili na danne hakki da rinjayar da karya.

Abin bakin ciki, da yawa muna ganin yadda ake rantsuwa da Allah bisa karya da zalunci domin a yardar da mutane ko a taushe wadansu, a karshe mai rantsuwar ya yi mutuwar fuju’a, kwatsam ya je ya iske azaba a kan azaba, domin ya dandani sakamakon mugun aikinsa. Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da yaudara, sai dai (ku ci dukiyar) idan ya kasance daga fatauci ne bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada ku kashe kanku. Lallai ne Allah Ya kasance game da ku, Mai jin kai ne. Wanda ya aikata wancan bisa ta’adi da zalunci, to za Mu kone shi da wuta. Kuma wannan ya kasance ga Allah (abu ne) mai sauki.” (Nisa’i: 29-30).

Kuma Mai tsira da amincin Allah ya ce: “Wanda ya ci wani yanki na dukiyar Musulmi da rantsuwar karya zai hadu da Allah Yana mai fushi da shi. Sa’an nan ya karanta daga Littafin Allah Wanda ambatonSa ya girmama: “Lallai ne wadanda suke sayar da alkawarin Allah da rantsuwoyinsu da ’yan tamani (kudi) kadan ba su da rabo a Lahira, kuma Allah ba zai yi musu magana ba, kuma ba zai dube su (dubar rahama) ba, kuma ba zai tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai radadi.” (Muttafakun alaihi).

Ana kiran yin rantsuwa bisa fajirci da zalunci da rantsuwar cakudawa wadda take cakuda ma’abucinta a cikin zunubi sannan ta cakuda shi a wutar Jahannama, Allah Ya yi mana tsari.  Buhari (Rahimahullahu) ya kulla wani Babi a cikin Sahihinsa da ya kira Babin Rantsuwar Cakudawa, sannan ya ambaci fadin Allah Madaukaki: “Kada ku riki rantsuwoyinku abin yaudara a tsakaninku har kafafu su zame a bayan tabbatarsu domin ku dandani munin abin da kuka toshe a tafarkin Allah, kuma kuna da azaba mai girma.”

An karbo daga Abdullahi bin Amru (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai ku kuna kawo husuma zuwa gare ni, abin sani ni mutum ne. La’alla waninku ya fi wani iya baki. Idan na yi hukunci na ba wa wani hakkin dan uwansa, to, wancan din ya sani yanki ne na wuta na yanka masa, don haka kada ya karbi komai daga gare shi (ya guji hakan).” Tirmizi ya ruwaito kuma ya ce Hadisi ne mai kyau ingantacce.