Wani sojan bogi ya shiga hannun ’yan sanda a Jihar Ogun bayan da ’yan sanda suka kama shi tare da wadansu da ake zargin masu laifi na.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa, dubun sojin bogin mai suna Jolly Gilbert ta cika ne bayan da jami’an rundunar suka yi wa wadansu da ake zargin batagari ne dirar mikiya. “Da jami’anmu suka kama shi tare da wadansu da ake zargin batagari ne ya ce shi soji ne da ke aiki da bataliya ta 174, da muka tuntubi jami’an sojin da ke aiki da bataliyar bayan sun gudanar da bincike sun shaida mana ba soja ba ne inda muka tsare shi muka ci gaba da gudanar da bincike,” inji shi.
An tasa keyar sojin bogin zuwa sashin yaki da manyyan laifuffuka (SARS) inda ake ci gaba da bincikarsa kafin a gabatar da shi ya fuskanci shari’a. A ’yan kwanakin nan ana yawan samun masu aikata laifuffuka wadanda suke yin amfani da kayan sarki na soja a jihar.