Walwalin-waliyon walankeluwa
Adon takun waiwayawa
Ina kuke Haurobiyawa
Miyagu sun yi yawa
Dukiya akai wa yankar ciyawa
kullutun kuraje
kafa mai kaushin kauje
Nadi na nan tattare da lauje
A zo komai a baje
Kar a zo ana mana jaje
Uwargidan asusu
Kinkimi-Adadun Asusu
Kar ki taimaki aikin kusu
Don an yi kurmusu
Ko taron shasha da sususu
Batun Gwarzon gwaraza
Kurarsa tai gaza
Ya tunkari karzaza
Mai borin barhaza
Da yai ta’asar banza
Masu warwaso
Sun taka rawar koroso
Talaka na kwana a keso
Ba wankan sabulu da soso
An bar shi da rikon kwankwaso
Tatasai dan damaso
Tunkuzar mai na ta naso
Ana ta kaso-kaso
Masai wajen wasan kyankyaso
Cututtuka sun diddiso
Gizo-gizon dakin gwaggo
Dubi wulwulawar agogo
Ka kori farin dango
dimbin hatsi suka zazzago
Ba ka da sabo na bayan kango
Mai taguwa da maho
Ka daina busa kaho
Ko cunkusa Hauro a baho
Gudun kar ka biya lanho
Haka makirai ke tunkaho
Surar dan tsako sai shaho
Aikin ga sai a ce hohoho
Sakon ga aike shi ta tarho
Wadanda sun ka jiya a nuho
Wato kowa ya taho
Girkin nauyaya-niyya
Gararumar gyaran jar-miya
Gudunmuwar ’yan jam’iyya
Gangamin sharar tsintsiya
Ga dan boton masu tsiya-tsiya
A fallen sabon babi
Kowane shafi a bi
Ai ta karatun adabi
Daga gobe zuwa jibi
Kyawawan ta’adu ne da kanbi
Gwamna Lalong
dan uwan Mista Darlong
Ku yi mana aikin Mao Zedong
Ko kafa kantin Dong fong
Al’umma tai kasuwanci a shagong
Aikinta ya zarta na Di-jango
Wanda hargitsa Filfilon toto
Miyagu sun yi wa juna kwanto
Babu mai musu kwarmato
Lalong ka karya musu lago
Mahtma Gandi
Indiyawan Indira Gandi
Suna da dabbobi masu bindi
Makiyayar garke ba adadi
Ana kai-kawo har Lahadi
Japanawan Hirohito
Sun firfito
Kun ji ’ya’yan Abe
Kun fi karfin babe
Ku bai wa kurciya koto
Samfarerar Tayar-Landan
An santa a birnin Lantsandan
Mun tauna ’yar kadan
Liman da Ladan
Ku karo du’a’in
An yaba wa juna kashin kaji
Artabun Wargaji da Gogaji
Ban da karbar ’yan kunji-kunji
Ko a nausa kungurmin daji
Ai tubus an gaji
Ni ne Dodong
Zan sa yi wandong
Tsibin kaya a kwandong
Ko za a sayar wa Gizagong
Sai ya fito daga kangong
Mu zauna sumul kalau
Ban da harbin ja-ni talau
Dankon gwafa kakau
Ana ta musayar miyau
babatu babu kyau
Tabargazar Tarba-tarba
An sanya mata takaba
Aya kuwa zakinta an yaba
Wannan babu tababa
Batun ingarma babu makuba
A hau bisa kan turba
Mu daina gaba
Da giba
Turnukun daba
Ai ba a samun galaba
Wannan batu ne a kan gaba
A tantance tsakuwa da tsaba
’Ya’yan Inna da Baba
Wasu sun sha romon jaba
Sun yi wa rayuka kakkaba
Junanmu na bukatar tuntuba
A daina jibgo karya a yaba
Rabin rabun rababa
Jibgin jiba
Da man dangwali yaba
babatun baudiyya
buruntun barauniya
Sakarcin sukuwar godiya
dumamar yanayin dirkaniya
Rukukin rarakar rafkiya
A daura kyakkyawar aniya
Fullo ga makekekiyar makiyaya
In gayauna Tai yabanya
Hatsi mu auna tiya-tiya
Mu kiwata tsuntsun miya
Bisashe su yawaita
Tumakai
Da awakai
Rakuma da alfadarai da jakkai
Nagge ko karsana a turketa
Kajin zakaru na da akurki
Ga kwayaye da ’yan tsaki
Tantabaru ai musu dan daki
Gandun daji a bar wa su zaki
Aura da daurin mangalar taiki
Ai wa shuka ciron haki
A rambada mata taki
A samu yabanyar mamaki
Kowa ya dukufa da aiki
A tsara komai daki-daki
Haurobiyawa
Mu farmaki masu garkuwa
Da ke sanya al’umma tsuwwa
Kai ai musu tsawa
Kashe fatari ya jawo hargowa
’Yan iska masu dagawa
Da suka tare a kungurmin dawa
A koya musu shukar dawa
Ta’asarsu ta rage hauhawa
Ko su tunkari giwa
Al’umma da tai juriya
Dogewar dauriya
Sai tai murmushi da dariya
Himma dai mutan Haurobiya
Kar mu yarda da wariya
Sabuwar shekarar masu kishi
Gyaran kasa ba fashi
Tarinnmu ya zam kwasar dashi
Mui kiyaye dokoki kowane sashi
Sai mu kalli juna da gashi
Na ci muku albasa mailawashi
Mu kafa wa kasarmu harsashi
Kowa ya daina jin haushi
Mu biya wa juna bashi
kururunmu yai dundum da koshi